YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 13 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 13 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 13 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA Can sai aka hango wani mutum ya keto fili a kan doki ga Waziri biye da shi tare da wani kyakkyawan saurayi. Kuma shi wannan mahayi ya rufe fuskarsa, sai idanunsa kawai ake iya hangowa. Mutane sai suka rika zaton cewa wannan lallai wani babban amini ne na masarautar ya halarci wurin nadin Sarki, shi ma sabon Sarki haka ya ke zato. Saboda haka nan da nan aka ba shi kujera ya zauna a cikin tantin da Sarki ya ke. Albarkacinsa shi ma Bashari ya sami zama cikin wannan babbar inuwa. Ita ko Bingyel ‘yar Fulani da ke can cikin taro da ta hango saurayinta sai ta fara tsalle tana daga hannu wai ko zai hangota, amma ina, saboda yawan jama’a. ZAMU TASHI Sarkin Fulani ya tambaye ta dalilin daga hannunta, sai ta ce, “Dubi babban bakon can da ya zo yanzu, kusa da shi wane ne zaune?” Dattijo ya kyalla ido sosai, ya ce, “Ai kuwa Bashari ne, yaya aka yi ya sami zama cikin sarakuna?” Bayan an kintsa…