YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 12 BY HARUNA USMAN

YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 12 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER  12 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng  A JIYA MUN TSAYA To yadda al’adar mutanen garin ta ke, in Sarki ya rasu, sai an yi watanni uku sannan za a nada wani. Haka al’amarin ya kasance, wato sai aka shiga jira tare da ‘yan shiryeshiryen da suka dace kafin zuwan lokaci. . Amma shi Bashari sai ya ci gaba da tafiya yana jiyyar Sarki gwargwadon iyawarsa da dan abubuwan da ya sani har Allah Ya kawo shi wata riga ta Fulani. Aka kai shi wurin Sarkin Fulani wanda ake kira Ardo Jumare, wani dattijo mai farin gemu da yawan shekaru. Bashari ya yi gaisuwa cikin ladabi da girmamawa, sai Ardon ya tambaye shi labarinsu, amma tsoron rashin sanin wadanne irin mutane ne zai sake haduwa da su, da kuma tunanin in ya fadi gaskiya labari na iya komawa kunnen wadancan mutane su sake zagayowa su halaka su, sai Bashari ya ce, “Mu fatake ne ‘yan kasuwa ni da mahaifina, sai na nemi izininsa don zuwa in wanke rigata wadda ta yi dauda, ZAMU TASHI ‘yan fashi suka far…