YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 15 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 15 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 15 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Sai dai kash, akwai wani abu da ke matukar damun su a tsibirin. Wato wani irin dodo ne, shi ba mutum ba shi kuma ba dabba ba. Kansa kawai ya kai girman akawalin doki, kuma yana da idanu hudu, daya a goshi, daya a keya, daya a kasan kunnensa na dama dayan kuma a saman kunnensa na hagu. Kowane kunne ya fi matsakaiciyar tabarma fadi kuma yana da bakuna guda biyu, daya a baya dayan kuma a gaba, kuma kowane baki zai iya hadiye Kato komai girmansa. Wannan dodo dai yana da hannaye guda hudu wanda kowanne yana iya daukar babban dutse da shi, kafafuwansa kuwa kamar wasu manyan itatuwan rimi, cikin sa Kato wanda ko da wasa ba za a iya misaltawa da na toron giwa ba. Jikinsa kuma rabi da gashi daya rabin kuma babu, sannan yana wani irin doyi mai tsananin tayar da hankali. Ba kananan dabbobi irinsu kaji, talo-talo da awaki ba, kai hatta dawaki da rakuma in suka ji doyinsa ba duka ne suke rayuwa ba. A…