YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 18 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 18 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 18 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA saboda tsananin kwarewa sai ya goce ya fado daga kujerar da ya ke zaune. Takobinta ya soki kujerar, kuma duk da kasancewar kujerar ta dunkulallen bakin karfe amma sai da takobin ya huda ta, kuma saboda tsananin dafin takobin da sihirin da ke jikinsa sai ga kujerar tana zagwanyewa, Karfe na narkewa kamar kankara. Nan da nan fada ya kaure aka yi kaca-kaca da kayan da ke cikin fadar don tsananin gumurzu, babu shakka Idrisu ya san cewa Sarauniya jaruma ce. FADA ya yi fada tsakanin jarumi Idrisu da Sarauniya Zinkadaziyya, ita tana Kokarin samun sa a makasa ta aike da shi lahira shi kuma yana KoKarin takura ta, don ya kama ta ya daure, kasancewar shi ko kadan ba ya bukatar kashe ta, shi ya sa ma ko takobinsa bai fitar ba. Tun daga cikin fada har sai da suka yiwo waje suna ta gwabzawa. Babu shakka wannan Sarauniya ta fi Karfin a kama da hannu, ko da a wurin irinsu Idrisu din, don …