YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 5 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA CHAPTER 5 BY HARUNA USMAN
YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 5 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA lallai dakin ya kasance ma‘abucin fitilu masu haske a bayansa don ya rika haska musu wasanninsu. Yana so kuma a kammala wannan aiki ne a cikin kwanaki uku. Kartin aljanun nan suka ce an gama sannan suka bace. Wata rana suna zaune suna tsotson tatsattsun kayan marmari, shi kuma Sarkin aljanu yana kashingide a kan kilishi, wato kwana uku ke nan da ba da wancan umurni, sai suka ji wata irin rugumniya, aljanun nan sun dawo. Suka zo suka fadi suka yi gaisuwa tare da ZAMU TASHI cewa ga lambun nan ya shiryu. Sarkin aljanu ya cewa ‘yan mata su leKa ga lambunsu can an gama, suka tashi tare da shi suka je taga suna leKawa, sai ga lambu an ajiye shi a gefe shirim, kuma abin mamaki shi ne babu abin da babu irin na lambu a ciki. Shi wannan lambu dai da bakin Karfe aka yi shi, daga baya kuma aka cika shi da wani irin rairayi mai launi iri-iri. Itatuwa kuwa har da irin wadanda ba su sani ba ak…