YAKANA BOOK 2 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR KARSHE THEND
YAKANA BOOK 2 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR KARSHE THEND
YAKANA BOOK 2 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR KARSHE THEND Www.bankinhausanovels.com.ng suka hada a bayan ran marigayiya Hadiza, wadda har gobe, jibi, har gata basu daina yi mata addu’a ba. Dr. Sulaiman yana Abuja, sai week end yake zuwa musu, sai ko in duk sun samu hutu suma su ke bin shi. Ranar wata litinin kwana daya da tafiyar Sulaiman nakuda ta kama Fati, suka nufi asibiti ita da Alti, yaran duk suna Karkasara. Kafin magariba ta haifi sankacecen danta mai kama da Baban shi har farcen kafa. Sai waya Dr. Surayyah ta yi mishi cewa baby ya iso. Sai ga shi a washegari kamar an jefo shi, ya tadda Fati da baby a ‘aminity’, sai dai dakin cike yake da ‘yan uwanta. Sai daga nesa yake jifanta da murmushin ‘bani da abin da zan gode miki’. Ita ma murmushin take masa da su kadai suka san ma’anar abin su. Ba da son ranshi ba Yaya ta wuce da ita gida inda za ta yi wanka, don Alti an aiko mata rasuwar danta a kauyen su Kukawa, don haka za ta tafi a washegari. Dakin ta na da Yaya ta gyara mata su…