YAKANA BOOK 2 CHAPTER 1 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
YAKANA BOOK 2 CHAPTER 1 BY SUMAYYAH ABDULKADIR Karfe goma sha dayan dare garin Kano ya yi tsit, sai iskar hunturu da ke kadawa. Malam Ja’afar ya dauko tabarmar sa ya shigo cikin gida daga soron kofar gida. Zai gifta ta dakin Fati ya jiyo shesshekar kukan ta, ya dakata ya daga labulen yana kallon ta, tana zaune a kan darduma ta kunshe fuskar ta cikin hijabi sai kuka take. Ya karasa shigowa cikin dakin ya ce, “Fadimatu kukan me kike yi?” A razane ta cira kai ta dube shi idanunta jawur, sun yi luhu-luhu alamar ta yi kuka har ta gode Allah. Malam Ja’afar ya zauna a wata ‘yar kujera da ke dakin yana fuskantar diyar sa. Nanah ta soma motsi alamun za ta tashi daga barcinta, ta soma ritriga ta. Ya jima bai yi magana ba sai da Nana ta koma barcin ta ya ce, “Gaya min damuwar ki Fadimatu, ni mahaifin ki ne”. Ta share idon ta da hankici, ta ja shessheka kafin ta ce, “Baba babu komi”. Ya jima yana kallon ta, sannan ya yi murmushi ya ce, “Kina tuhumar mu da yi miki auren da baki so, auren mijin ‘ya…