WA ZAI FURTA COMPLETE BY ZAINAB WOWO
WA ZAI FURTA COMPLETE BY ZAINAB WOWO Www.bankinhausanovels.com.ng Gaba daya labarin tukuici ne ga Hajiya Rabi badawi ( maman Ibrahim ) Allah ya shirya Miki zuri’a ya Kara arziki Aunty Rabi tawa* *KINA RAINA MAMAN WEEDAD MARUBUCIYAR ALJAZEERA DA DR. JUNAID.* *FARKO* *Federal University dutsinma* Gudu-gudu, sauri-sauri take tafiya Babu abinda kirjinta keyi sai dukan tara-tara, dodazon mutanen dake chunkushe bakin gate wadanda security suka dakatar don bincike saboda Babu dalibin dake wucewa wurin sai ya gwada I D card, takaici da karuwar faduwar gaban suka Hana ta sukuni, sakamakon yaune ranar farko da zata Fara shiga aji a makarantar. Tana cikiniyar wucewa taji an janyo hijabinta alamar an mayar da ita baya Shi Kuma ya wuce da sauri Yana faman daga ID card din nasa, ta bishi da kallo saurayi ne matashi dogo….. *Anwar! Anwar !!* Wani ya bi bayansa da gudu, dai dai ta nuna nata ID card din ta wuce Shi Kuma ya juyo don ganin Mai kiransa har lokacin bai tsaya daga saurin da yak…