WA NAKE SO CHAPTER 17

WA NAKE SO CHAPTER 17
WA NAKE SO CHAPTER 17 Www.bankinhausanovels.com.ng  Shiru Aisha tayi. Abbah yace “Aisha tashi ku shiga.” Mikewa tayi gaban ta na faduwa tana tunanin tayaya zata shiga bandaki tare da mutumin da ba muharammin ta ba. Akan keken suka daura shi ya kara kama hannun ta yana kallon ta sannan nurse ta fara turawa a haka suka karasa bandakin.+ Katon bandaki ne wanda yake da sink da bath sai labule da ya raba wajen daya bangaren wajen shit. Ciki suka shiga dashi suka fara cire masa riga ido ta runtse. Daya ya fara hada masa ruwan wankan daya ya dauki tooth brush din sa ya saka masa toothpaste. “Gashi!” Nurse din ya fadawa Aisha. Ido ta bude taga yana miko mata brush din sa amsa tayi ta dago ta ganshi zaune da gajeren wando da singlet iso ta runtse da sauri ta mika masa amsa yayi yana kallon ta wani nurse ya matsa dashi ya wanke bakin sa sannan ya saka shi a cikin bath din juyawa tayi zata fita yace “Aysherrrr! wani irin yar taji a jikin ta wanda yasa ta saurin tsayawa bata juyo ba yace “Dan Allah kada k…