WA NAKE SO CHAPTER 15

WA NAKE SO CHAPTER 15
WA NAKE SO CHAPTER 15 Www.bankinhausanovels.com.ng  Zaune take a office din nata tana duba wani littafi dake gaban ta bayan tayi round ta dawo. Wayar tace ta dau kara tana dubawa taga sabuwar number. Dauka tayi tayi sallama. Amsawa akai sannan akace “Doctor An tashi lafiya ya kike ya aiki?”+ “Alhamdulillah amman ban gane waye ba?” “Jannah ce!” “Oh Jannah ya kike ya gida ina Noor?” “Gata!” Ta amshi wayar tace “Ina kwana ya aiki?” “Alhamdulillah ya gida da Hajiya?” “Tana lafiya!” “To agaishe ta!” “Zata ji.” “Aha nagode!” Jannah ta amshi wayar tace “Doctor ranar friday zan shigo muje radio station tare.” “To shikenan sai kinzo!” “Yauwah nagode ki gaida Momy.” “Zataji sai anjima!” Ta fada tana kashe wayar. Ido ta lumshe tana murmushi take ta tuna zuwan su gidan. Kenan su Noor yayan wannan mutumin ne Uncle wa ma taji suna cewa? Ohoo ta manta. 4:00pm Aka shigo office din ta da sallama. Dagowa tayi tana amsa sallamar Aslam ne ya fara shigowa ya kura mata ido,  kai ta dauke tana kallon system din gaban ta. Dagowa …