WA NAKE SO CHAPTER 14
WA NAKE SO CHAPTER 14 Tana fita ta hau kan titi tana driving tana dan girgirza kan ta domin yadda Hajiyar Fu’ad ke son ta har tausayi take bata. Take ta cije leben ta tana fadin “Amman ban kyauta mata ba sam dan ni Ya tafi ya bar mahaifiyarsa. Mace mai hakuri karamci da mutunci Allah ka dawo mata da Fu’ad cikin gaggawa kasa yana lafiya.”+ Kwallar da ta taru a idon ta tasa hannu ta goge ta. Idon tane ya sauka akan wajen da ake gashin kaji. Sanin Momy naso yasa ta matsa gefe tayi parking sannan ta danna horn. Nan da nan yaran wajen suka karaso. Ya leka ta window da ta sauke ta fada masa ayi mata parkaging guda uku sannan ya tafi da sauri. Ba ayi minti biyar ba ya dawo da babbar leda ya mika mata. Amsa tayi tace “But is like is more than three?” Ta fada tana budewa. “Yes Ma!” Kallon sa tayi tace “Why?” Nuni yai nata dashi da ya fito daga wajen dagowa tayi dan taga me ake nuna mata daga kafar sa ta fara kallon sa wacce take fara tas tai kyau a cikin bakin takalmin da ya saka. Sau Ash kalar wando …