ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 1 by Sumayyah Abdul-kadir

ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 1 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN BOOK 2 CHAPTER 1   by Sumayyah Abdul-kadir Washe gari muka raka Momi bikin walimar ‘yar aminiyarta Dacta Ladi, cikin Tudun-Wada. Lancin din da aka yi na ‘yammata a (Congo Conference) ya taimaka ainun wurin rage mana damuwa dukkanmu, kowaccenmu ba ta dawo haka ba sai da saurayi. Suka biyo mu har gida, Momi ce ta lal labasu ta ce su dawo gobe lokacin magariba ta yi ido na ganin ido ya fi. Washe gari kuwa da safe muka tattara muka koma Kaduna.  Har muka kare satin ni da Zanirah kowanne ya kasa_ sakin jiki da dan’uwansa. Abin da bamu taba tunani ko a mafarki zai taba faruwa a rayuwarmu ba. Kai SO din nan bala’i ne, masifa ne ba karama ba tunda har ya iya farraka (shiga tsakanin) ni, Ummi da Zanirah.  Ranar da zamu koma makaranta mun shirya tsaf cikin uniform. A bakin gate zan shiga motar Baban Kaduna ya ajiye ni makaranta, ita kuma za ta shiga school bus direban Baban ya maida ta Giwa (GGSS Giwa) sai ta riko hannuna. Ta matse gam cikin nata, hawaye ya fito daga idanunta ta yi a…