YAKANA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
YAKANA BOOK 1 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR tare, har yanzu bani da lafiya”. Da gudu suka mike daga jikinta suka nufi dakin su suna murnar zuwan Antin su da suke tsananin so. Alti ta yi sallama dauke da tray kanta a sunkuye ta ce da Hadiza, “Na ce sai na daina daura abinci a tebir?’ Hadiza ta yi murmushi mai hade da wani irin huci mai zafi, ta ce, “Idan maigidan yana son hawa tebir din fa?” Ta fada tana kallon Sulaiman. Bai dago ya kalle su ba, haka bai tofa musu ba, duk da ya lura ta bakinsa suke son ji. Alti ta ajiye katon tray a gaban Hadiza ta juya ta fita. Tana ba da baya ya suri Hadiza a kafadar shi sai dakin barcin su. A hankali ya sauke ta a makeken ‘family bed’ din su, ya koma toilet ya cika baf da ruwa mai dumi, ya zuba dettol kadan ya dawo ya soma warwarewa Hadiza kayan jikinta, ya nade ta cikin towel ya sake sungumar ta ya yi toilet ya sanya ta cikin ruwan da ya hada. Ita karfin Sulaiman mamaki yake bata. Ya yi mata kyakkyawan wanka da kamsassan sabulun Zest, ya nado ta …