WA NAKE SO CHAPTER 10

WA NAKE SO CHAPTER 10
WA NAKE SO CHAPTER 10 Tin daga lokacin kuma Momy ke kula dani sosai dan bata bari na na zauna ni kadai kullum cikin min abinda zai dauken kewa suke ita da Yaa Kamal dan Suraiyya ta shiga busy rabon invitation card. Samun kulawa a gun Momy sai ya kwantar min da hankali sosai dan ban fiya sa tunani ba sai dai in naje bacci da kyar nake yi saboda tunanin Fu’ad ga zuciya ta dake ta min zafi da radadi wanda na rasa saboda me duk maganin da nake sha a banza.+ Wani lokacin sai na sha maganin bacci nake samun da kyar baccin ya dauke ni sam bani da kwanciyyar hankali na rame sosai. Son Fu’ad ke dawainiyya dani. Ga kewar sa. Muryar sa kadai nake son naji amman ba hali duk na shiga tashin hankali. Yau tin da na tashi da wata kewar sa na tashi wanda ji nake in banga Fu’ad ba ba zan iya kaiwa ba. Sosai hankali na ya tashi fa da gaske ji nake kawai ni shi din nake son gani ko ta halin ka’ka. Tunani na fara shin ni a ina zan ga Fu’ad bayan kullum sai na kira wayar sa sau ba adadi amman a kashe. hajiyar …