UNCLE NE CHAPTER 4 BY NIMCYLUV
baki iya neman permission ba ko?” ya Æ™are maganar yana ware É—aurin da Mummy tayiwa sumar kanta,turo baki gaba tayi cikin Muryar shagwaÉ“a tace “zafi fa” waro idanu yyi waje tare da faÉ—in “where?” hannu tasa ta nuna dwon lips É—inta inda ya murÉ—e mata, bai ce mata komai ba sai sumar kanta da yabi da kallo,harga Allah yana
Æ™aunar yaga suma mai yawa shiyasa a karan kansa ba bai fiye cire tasa ba,matsawa yyi can gefe tare da zama saman sofa yaci gaba da kallon tafsir a sunna t.v, haÉ—e rai yyi sosai kamar ba shine yyi mgn yanzu ba,ganin hakan yasa ta kwaÉ“e fuska tare da juyawa zata bar É—akin..,cikin Æ™asa da murya kamar mai raÉ—a yace “kee ubanwa zai zuban?” ya Æ™arasa tambayar yana Æ™ara maida hankalinsa ga tafsir É—in da ake,tsaye tayi masa aka after 20 seconds ta Æ™arasu wajan zata taÉ“a jug É—in taji saukar muryarsa yana faÉ—in “out..!” yadda yyi maganar yana É—aga murya yasa ta tsorata dashi,da sauri tabar É—akin jikinta duka rawa yake,tana fita ta haÉ—u da Aryan zai shiga side É—insa da gudu ta faÉ—a jikinsa ta saki kuka,bayanta ya shiga bubbugawa tare da shafa sumar kanta yace “stop cry beb..and keda wa kike kuka?” ya tambaye ta tare dasa hannu ya fara goge mata hawayen dake saman fuskarta,shuru tayi masa ba tare da tace komai ba, attention É—insa ya Æ™ara mayarwa kanta yace ” you refused to answer my question,keda waye beb?” Æ™ara shagwaÉ“e fuska tayi tace “uncle ne,ina jin tsoron sa” dry yyi mata yana jan hancinta yace “ehyeee keda uncle É—in naki” baya ta juya masa tana Æ™ara matso hawayen idanunta ,ganin baice mata komai ba yasa ta fashe da kuka tana buga leg É—inta a Æ™asan tarazo,da sauri ya matsu kusanta ya jawota zuwa jikinsa yace “ohhh sorry beb, kin san uncle bai son hayaniya,kuma bai son magana biyu saiki kiyaye” kaita É—aga masa alamar “to” murmushi yyi mata yace “good gril,maza jeki ga Nihila can ta dawo” jin hakan yasa ta sake sa da sauri ta nufi parlour’n,tana zuwa taga Nihila zaune kusa da Mameey jikinta ta faÉ—a tace “wlcm sister” dry Nihila tayi tace “Thank You dear,muje kiji wata magana” tana faÉ—in haka taja hannunta zuwa upstrais,da dry Mummy da Mameey suka bisu, Mama kam na Æ™wance da rubar ice cream kusa da ita a haka tayi bacci, yana zaune saman sofa yana speading coffee a bakinsa,ya É—ura leg É—insa saman table É—in time to time yakan lumshe idanunsa tare da fesar da numfashi ta bakinsa,a haka ya samu ya shanye 1 cup na coffee É—in,yana nan zaune idanu lumshe Jafar yyi sallama ya shigo,ware idanunsa yyi ya saukesu aÆ™an Jafar daya zauna gefen sa tare da tsiyayar coffee a cup ya fara sha,É“ata rai Jalal yyi kamar wanda akaiwa dole yace “why zaka shigo min without my permission?” dry Jafar yyi tare da É—auka remote ya sauya channel É—in zuwa zee world, ya fara kallon series É—in twist of fate “ni nasan ba aure gareka ba,bare nayi tunanin idan na shigo babu izininka zanga abinda bai dace ba” banza Jalal yyi masa har sai da ya gama surutunsa kana yace “yunwa fa na keji,dan naga kai kamar azumi kake” still nan ma Jalal bai kula sa ba,sai É—aukan remote da yyi ya sauya channel,tsaki Jafar yace “wannan ai rainin hankali ne,kai kake kallon ko ni?,da zaka sauyamin” sai a lokacin Jalal ya buÉ—e idanunsa tare da saukeso akan Jafar,iska ya fesar kana ya Æ™ara lafewa jikin sofar,some minutes ya Æ™ara kallon Jafar yace “ina son zama president of ibadan what is ur opinion?” zare idanu Jafar yyi yace “are you mad? kasan me kace kuwa shugaba Æ™asa fa Jalal” gira guda É—aya ya É—aga masa tare da É—aga shoulders É—insa tare da ware su alamar “so what..!?” jinjina kai Jafar yyi tare da kallon Jalal sosai yace “look Jafar you can do what ever you want to do,but zama president ba sauÆ™i,and kuma kasan wanene president Mubarak Yahya cibo kowa,kana sane da cewa dukkan wanda ya haÉ—a takara dashi sai dai wani bashi ba,idan kai baka son rayuwarka to aÆ™wai masu buÆ™atar ta just like me, please Jalal forget all think kayi farcing rayuwarka na gaba” ya Æ™are maganar cikin sigar lallashi..,” kallo É—aya bobo yyiwa Jafar ya É—auke kai kafin yaja ajjiyar zuciya yace “kasan mene cikar buri?” cikin É“acin rai Jafar ya miÆ™e tsaye yace “ban sani ba sai kai faÉ—an,wlh saina ha É—aka da Abbou yanzu ma dan ance baya nanne,but i will be back in sha Allah” bai ko tankasa ba bare ya saka ran zai ce masa wani abu,a haka harya fice daga part É—in nasu,a main parlour yaga Nihila zaune ita da Jalilerh “a’a beb keda Æ´ar wajan Jalal ce” murmushi Nihila tayi masa tare da sunkuyar da kai Æ™asa sabida kallon da yake mata,sofa ya samu ya zauna tare da Æ™walla kiran sunan Mummy yana Æ™oÆ™arin Æ™ara kiran Mummy yaji an rafka sallati a bayansa ana faÉ—in” Muhammadu Rasulullah (s.a.w) amma kai dai Jafaru baka tsoran Allah,yanzu sabida tsabar rashin mutunci da mugun hali irin na yaran zamani sai da ka tasheni a baccin nan,huuu ina ganinka na kirki ashe kaima tantirin bugawa a jarida ne kamar abokin naka..,wlh ku sauya hali domin aure zakuyi babu gantalalliyar yarinyar da zata zauna da ko a haka” ta Æ™are maganar tana tura rubar ice cream É—in dake kusanta a baki kana ta É—ura da faÉ—in “kai wannan abu ba dai zaÆ™i ba, duk yadda akai an zuba kindirmo a cikin wannan abun.,ai Jafaru ban baka labari ba ina sane É—azo na faki idon wancan misalin na É—auke rubar wannan kindirmon” tunda ta fara magana Jafar yake dry,domin shi karaÉ—inta dry yake basa, Nihila tace “aikam yanzu naji kuma saina faÉ—a masa” miÆ™ewa Mama tayi tsaye tace “yooo ke daman ai baki tsoran Allah,ban taÉ“a ganin yarinya mai baÆ™in jini irinki ba,har yanzu babu wani mashinshi ni..,” da sauri Jafar ya dakatar da Mama ta hanyar faÉ—in “a’a Mama nifa? bayan kin san ni nake riÆ™o” taÉ“e baki tayi tace “kaji dashi nidai nayi nan” tana tafiya Mummy na sakkowa daga upstrais zama tayi kusa da Jalilerh wacce take bacci saman sofa tace “a’a son kaine a gidan namu” sunkuyawa yyi yace “eh mummy na sameku lfy” murmushi tayi tace “lfy lou” kallon bayansa tayi tace “ma sha Allah” kai ya sosa yace “Mummy am hungry” dry tayi masa kana ta kalli Nihila wacce ke danna wayar Mameey tace “beb jeki kawo masa abinci” ta faÉ—i hakan tana kallon Jafar kana tace “shi bobo yana ina?” dry yyi shima yace “kin san halinsa Mummy ai,yana can part É—insa” jinjina kai tayi kana ta miÆ™e ta nufi part É—in nasa.
a zaune Mummy ta samu Jalal ya lumshe idanunsa yana tunani gefe guda kuma,t.v nata Æ™ara ita É—aya tana shiga ta sanya hannu ta É—auki remote ta kashe kallon,zama tayi kusan shi and she start staring at him for some minutes, numfashi ta sauke tare da kiran sunansa,tun shigowarta ya san itace ta shigo kawai bai son yin magana shiyasa baiko mutsa ba,sai yanzu data kira sunansa ya janye hannunsa on his face,idanu ya zuba mata kafin yaji ta É—ura hannunta a saman forehead nasa tace “Allahamdulillah nayi tunanin ciwonne” lumshe ido yyi tare da Æ™ara kallonta, miÆ™ewa tayi zuwa É—an Æ™aramin fregd É—in dake parlour’nsa, buÉ—ewa tayi taga tarkace da yawa, gashasshen kifin daya shigo dashi É—azo ta É—auka tare da É—aukan plat ta saka a ciki, ruwa ta É—auka mai sanyi da kuma apple itama ta saka a wani plat É—in,kana ta Æ™arasu inda yake zaune “rayuwa baza ta taÉ“a yiyuwa babu abinci ba bobo,sam baka damu da kanka ba,mutum sai ya wuni a É—aki dukkan abinda akace yyi na aiki yace bai so,kenan karatun ya tashi a banza” ta Æ™are maganar tana buÉ—e bakinsa tare da tura masa kifin,a hankali ya fara taunawa ba dan yana so ba,sai taga yaci sosai sannan ta bashi ruwan da kuma apple É—in.
washegari tun da safe ya fice daga gidan bai dawo ba sai wajan ƙarfe biyar na yamma yana shiga ya hango Jalilerh ƙwance tana bacci daga ita sai wani ƙaramin sket wanda iya kacinsa cinyarta sai kuma vest,baiko ƙara kallonta ba ya shige cikin part ɗinsa.
wajan sati guda kenan bobo baya samun zama,a haka harya samu zama da shugaban jam’iyyar kana aka bashi damar siyan Form na neman takara a take a wajan ya siyi Form É—in ya cike,kuma a ranar aka tabbatar dashi a É—an jam’iyyar D.R.P kuma mai neman kujerar shugaban Æ™asa,a gajiya ya shigo gidan yana shiga ya nufi part É—insa ya zare kayan jikinsa ya nufi bathroom taken shower yyi kana ya sanya wata milk É—in jallabiya mara nauyi, bayan ya shirya ya fito sai zabga Æ™amshin yake,kai tsaye part É—in Abbou ya nufa yana zuwa main parlour ya samu Mameey ita da Æ´an ukunta da kuma Mama sai zabga Shira suke,fuska ya sauya kana yyi gyaran murya yace “gida kamar club,zaku É—auki hakkin wasu fa” haÉ“a Mama ta riÆ™e tace “yau naga É—an nema,ni kake ma baÆ™in ciki sbd ina basu labarin kuruciyata,to wlh sai dai baÆ™in ciki ya kasheka” bai kula taba ya haura upstrais abinsa, tsayawa yyi baÆ™in Æ™ofar har sai da Abbou ya bashi damar shiga,yana shiga ya zame Æ™asan kujera kusa da Abbou yace “Barka da rana Abbou” murmushi Abbou yyi tare da ajjiye jaridar daily trust a gefen sa yace “bobo na sai na kejin labari daga sama,nida nake gidan banji ba,to ina maka addu’ar samun nasara Allah ya taimaka” sosai bobo yaji daÉ—in addu’ar Abbou domin abinda yake son sanar dashi kenan,cikin Æ™asa da murya yace “Abbou ka amince?” kansa ya shafa yace “tayaya zanÆ™i abinda gudan jinina keso? naji daÉ—i nayi farin ciki Allah ya nuna mana lokacin Election” da “Ameen” ya amsa kana ya miÆ™e ya nufi dwonstrais,yana gifta É—akin Nihila yaga inuwar mutum,a hankali ya fara takawa zuwa É—akin yana isa yaga Jalilerh tsaye bakin Æ™ofar hannunta riÆ™e da brezia,kallonta yyi yaga daga ita sai Æ™aramin towel sai rarraba idanu take,fuska ya haÉ—e yace “gulma ko?”turo baki tayi gaba tare da É—an buga Æ™afarta tace “ba kai ne ba” ware ido yyi waje tare da nuna kansa yace “me? ok where are you hiding?” fuska ta shagwaÉ“e tare da nuna masa brezia hannunta tace “wannan ne ban iya sawa ba,and kuma Mummy tace dole nasa” lumshe idanunsa yyi tare dasa hannu ya jawota zuwa gabansa kana ya juyata zuwa baya yace “muga” brezia ta bashi shi kuma ya amsa,waro ido waje yyi ganin number dake jikinta,baice komai ba ya É“alle bottle É—in dake jiki a hankali kuma ya saka hannunsa a gadon bayanta..
saurin juyowa tayi gabansa tare dasa hannunta a Æ™irjinsa cikin kwaÉ“e fuska ta kallesa tace “Uncle baka iya ba ai” lips É—inta ya Æ™orawa idanu,kafin yaja numfashi ya sakar mata brezia a Æ™asa,kana ya gyara tsaiwarsa kamar mai koyan magana yace “wake saka maki da?”turo baki tayi sai kuma ta saki dry tace “to aini bansawa” jinjina kai yyi yace “i see” bai Æ™ara kallonta ba ya juya yyi tafiyarsa,a main parlour ya samu samarin gidan da Mummy da Mameey da kuma Mama zaune tasa farfesun nama a gabanta,kallonsu yyi ya É—auke kai har yaje bakin part É—insu ya tsaya cikin Æ™asa da murya yace “time for paryer” yana faÉ—in hakan ya juya abinsa zuwa cikin part É—insa,yana shiga ana kiran sallar magrib, bathroom ya huce yyi wanka tare da É—aura al’wala,a parlour ya samu Abbou ya fito su Irfan kuma na jiransa,a jere suka nufi masallacin bayan sunje suka samu liman ya dawo dan haka Jalal bai Æ™arasa wajan tayar da sallar ba, murmushi Liman yyi yace “mu duka kai muke jira daman shekaruna sunja,bai ce komai yaje ya tayar da Sallah,bayan an idar Abbou ya buÆ™aci su tafi zai dawo,kallonsa Jalal yyi kamar mai son faÉ—in wani abu sai kawai yyi shuru ya miÆ™e suma sauran Æ´an uwansa suka bi bayansa,haka nan kawai ya samu kansa da faÉ—uwar gaba wacce bai san dalilin hakanma, suna tafe su Imran na shira shidai kawai jinsu yake da kunne, Irfan ne ya kallesa yace “yaya wlh ka shiga takara a Sa’a,domin jama’a suna sonka,daman tuni suka gaji da shugabancin zalunci da shugaban Æ™asa Mubarak Yahaya cibo,jiya na kunna data na kamar ance na shiga Twitter,ina shiga na fara ganin photonan ka na ibadan wasu da kayan likitoci wasu da kayan gida, jama’a sai mara maka baya suke” ya Æ™are maganar yana kallon yayan nasa wanda baice masa komai ba, Aryan ne ya É—ura da faÉ—in “nayi mamakin yadda jama’a suka samun wannan photonan wanda komu bamu dashi,ai in sha Allah daga wannan lokacin kashin President Mubarak Yahya cibo ya bushe,zai ga yadda ake mulki mai cike da tsafta da kuma adalci” lumshe idanunsa yyi tare da fesar da iska daga bakinsa kafin ya kalli ko wannansu yace “Jafar zai zo da paster” a haka suka Æ™arasa cikin gidan,suna shiga main parlour suka, zazzauna Jalal yasu shigewa part É—insa Mameey tayi saurin faÉ—in “bobo sai muke jin abin farin ciki, gsky nayi murna Æ™warai da gske, Allah ya taimaka ya kuma baka nasara” waje ya samu kusa da Mummy wacce ko inda yake bata kalla ba hakan ya tabbatar masa da fushi take dashi,bayan ya zauna ya kalli Mameey da murmushin sa na gefen baki yace “Ameen ya rabb Mameey na” hannunsa ya É—ura akan na Mummy wacce take latsa waya banza tayi masa, ganin hakan yasa ya Æ™wace wayar hannunta tare da shige jikinta, ajjiyar zuciya ya sauke kafin ya fesar da numfashi yace ” i missed You Mummyna,why kike fushi?” kallonsa tayi taga yadda ya faÉ—a idanunsa suka Æ™ara fitowa ga farin daya Æ™ara,rai É“ace tace “Muhammad tashi a jikina” zare jikinsa yyi domin tunda yaji ta ambaci sunansa yasan taje Æ™arshe wajan É“acin rai,yana tashi ta miÆ™e taja hannunsa har zuwa saman upstrais,da kallo su Aryan suka bisu banda Mameey wacce take murmushi daman tun É—azo take ganin Mummy a kumbure ashe ita da bobo ne, Mama taÉ“e baki tayi tace “ah to shi rikon maraya ai sai mai Æ™oÆ™ari,banda haka wacce gantalalliyar ce zata iya da wannan miskilin,mutum kamar wanda akaiwa AL’BISHIR da wani nasa ya mutu,yadda zuciya take a kumbure haka fuska take kamar zai fasa ihu..,ohhh wlh da bansan shi ba bazance Kabeeru ne ya haifi Wannan basa mudan ba” Mameey data san kan zancen taja bakinta tayi shuru,su Irfan kam da idanu kawai suke kallonta domin sam basu fahimci komai a zan can nata ba.
Mummy na shiga ta zaunar dashi a Æ™aramin parlour’n ta,bata Æ™ara kallon inda yake ba ta shiga kitchen É—in dake part É—in ta juna hiter tare da zuba kayan Æ™amshin,sai daya tafasa ta sauke,ta haÉ—a masa tea mai kauri wanda yaji bonvita da madara,plat ta É—auka ta cika masa shi da cips,cikin parlour’n ta dawo hannunta É—auke da tray,table ta jawo gabansa tare da ajjiyesa a saman table É—in,fuska a É—aure ta kallesa tace “eat,kada ka rage komai” kallonta kawai yyi harta fice daga parlour’n ta nufi cikin bedroom É—inta,ganin abincin gabansa ya sashi jin yunwar bawai dan yana so ba,shi sam bai san mene yasa abinci bai damesa ba,bai san mene yasa a duk sanda yaci abinci ya cika cikinsa ba ya kejin cikinsa nayi masa zafi,mararsa ta kumbura tana masa zugi,yana É—aya daga cikin abinda yasa bai son cin abincin,table É—in ya jawo gabansa tare saka spoon ya É—auki cips É—in yakai bakinsa,saurin lumshe idanunsa yyi sabida daÉ—in É—aya ziyarci kunansa,a hankali ya dinga cin cips É—in yana haÉ—awa da tea É—in gabansa,har sai da ya cinye tas,domin bai son ya karya mata rantsuwar da tayi,yana gamawa tana shigowa hannunta É—auke da wata damammiyar fura, zaro idanu waje yyi kana ya miÆ™e tare da kwaÉ“e fuska yace “Mummy i’m done” itama haÉ—e rai tayi duk da irin dariya da yaso bata,domin tasan ganin furar ya sashi miÆ™ewa, zaunar dashi tayi tare da zama kusansa tace “haa” tsuge bakinsa yyi ba tare da yace komai ba, ajjiye furar tayi ta kama hannunsa cikin nuna ta isa dashi da kuma nuna ita É—in uwace garesa tace.
“Rayuwa tana da sauÆ™i bobo,sannan kuma tana da wahala,a lokacin dakai kake tunanin abinda zakai mai sauÆ™i ne,wani a lokacin yake ganin mai wahala ne…,”tsayawa tayi da maganar tana kallonsa, idanunsa a rufe suke amma dukkan wani attention É—insa yana akanta, É—urawa tayi da faÉ—in.
“wani zai maka kallon maÆ™iyi,dalili kana son ka mallaki abinda yake dashi lokacin,da zarar kuma ka mallaka shi zai zama koma baya sabida burinsa da dukkan abinda yake samu ya na ga wannan abun daka rabashi dashi,hakan zai sanya yaga baÆ™inka yaga babu wanda ya tsana sama dakai,kuma zaiyi alwashi rabaka kaima da naka farin cikin kamar yadda ka rabashi da nasa,zai sadaukar da komai nasa in dai zai dawo da farin cikinsa..” tsayawa ta Æ™arayi sabida ajjiyar zuciyar da taji ya sauke, kansa ta shafa tace.
“ina jin tsoron abinda gaba zata haifar, Jalal bana son ganin wani abun ya sameka,kaine Garkuwa Nihila,nasan a yanzu ba zaka gane abinda nake nufi ba sai nan gaba,amma siyasa babu sauÆ™i kamar yadda kai kake tunani,kai muradin kai ne,shi kuma farin cikin sane,a naka tunanin mutum zai yarda ya rasa farin cikinsa ne..no! Jalal bazai taÉ“a yiyowa ba,zakai farin ciki a duk lokacin da kakeso,ina gaya maka wannan ne da nake a raye yanzu,wata rana bazan faÉ—a maka ba, aÆ™wai ranar daza tazo kayimin kallon muguwa ko azzaluma duk kana da hujjar da zakai hakan,amma hujjarka mutum biyu ne,bazan iya faÉ—a maka so ba sabida ni kaina ban sansu ba,amma dai an tabbatar min da hakan,kayi Æ™oÆ™arin kula da lafiyarka, domin wata rana mutum biyu kake da ikon riÆ™ewa kuma Æ™arÆ™ashin inuwarka..”
da sauri ya buɗe idanunsa ya ƙorawa Mummy idanu kamar mai nazartar maganarta, a hankali kuma yaja idanunsa ya rufe kamar mai yin bacci, murya can ƙasa yace.
“Ni duk kaina ya kulle, i don’t understand anything, mene kikayi da zanji zafinki,kinfi kowa sani i’m nothing without you,na tabbatar uwa ba zata taÉ“a cutar da yaronta ba,all i need for u,albarkarki”
Murmushi tayi masa kafin ta shafa sumar kansa tace “Allah yyi maka Albarka,ya baka dukkan abinda kakeso,ya baka sa’ar rayuwa data mutuwa,ya haÉ—a ka da mata nagari”
ya mutsa fuska yyi kafin ya miÆ™e tsaye, hugging yyi Mummy kafin yace “zani sallah” kansa ta sumbata kana ta sakeshi,ya juya ya fita daga cikin part É—in, yana zuwa yaga babu kowa a main parlour’n hakan tabbatar masa Abbou tun sallar magrib bai dawo gida ba,part É—insa ya shige direct bathroom ya huce yyi brush ya É—aura al’wala kana ya fesa parfume mai sanyi da daÉ—i,yana gamawa ya fita masjid, a compund na gidan ya samu Jafar dasu Imran suna kallon paster da Jafar yyi É—azo, photon Jalal ne yasha shadda sky blue da kuma hula dark blue, É—inkin riga da wando da kuma Babbar riga,sosai photon jikin paster yyi Æ™yau sabida murmushi gefen baki da Jalal yyi,daga saman paster an rubuta D.R.P Æ™asa sunan jam’iyyar an saka (power) daga Æ™asan paster an rubuta PRESIDENT MUHAMMAD JALAL BOBO, yana zuwa suka tafi wajansa suka rungomesa kansu ya shafa yace “darling” dry sukai gaba É—ayansu kafin a tare suce “we are proud of you yaya, munji daÉ—in samunka as brother” janyesu yyi daga jikinsa kafin ya kalli Jafar dake can wajan fanfo yana yin al’wala,yana gamawa ya matsu kusa dasu yace “wato ko dole sai kun nuna tare kukazo duniya ko?” dry Aryan yyi kafin yace “haba yaya Jafar,ai bamu sanin time É—in da muke magana tare” kai ya jinjina kana yace Irfan ya zura paster a cikin mota kafin su fito daga masallaci,suna shiga Masallaci su kaga ana rabon alwala da dabino haÉ—i da goro, Æ™arasa shiga sukai bayan an idar da sallah Jalal shima fitowa yyi bai zauna ba sabida cikinsa da yaji yana masa ciwo,yana fitowa waje yaji wasu suna faÉ—awa Abbou “to Alhaji Kabeeru Allah ya sanya alkairi..
ba tare daya kalleso ba,yyi shigewarsa cikin gidan,a main parlour ya samu Jafar zaune a kan sofa gefen sa kuma Nihila ce zaune tana duba littafi karatu sbd sun fara text ta second semester,waje ya nema can gefe ya É—auki wayarsa iphone 12 max ya fara latsawa, Jalilerh dake sakkowa daga saman upstrais ta Æ™arasu kusa dashi kanta a Æ™asa tace “uncle..!” kansa ya É—aga a hankali ya kalleta daga ita sai wata duguwar riga iya laps É—inta gashin kanta har baya,yana kallonta ya sunkuyar dakai Æ™asa ba tare kuma da yace komai ba,tana nan tsaye har Aryan ya fito daga cikin part É—insa,kallonta yyi yace “beb me kike a kansa?” fuska ta kwaÉ“e da sauri kuma ta Æ™arasa wajansa tace “chocolate Mummy yace nazo ta bani” murmushi yyi mata tare da kama hannunta yace “Mummy daman namiji ne?..idan macace haka za kice tace..,idan kuma namiji ne haka za kice yace” kaita É—aga masa kafin tasa hannunta a waist É—insa tace “yaya a kabani?” hancinta yaja yace “ok muje” daga gefen sa yaji Jalal yace “don’t go with her,and kada ka bata komai” yana faÉ—in hakan ya miÆ™e tsaye da saurin Nihila ta Æ™arasu wajansa tace “goodnight bobo” kanta ya shafa yace “night beb” ya faÉ—i hakan ya kissing kanta,hawayen da Jalilerh ke É“oyewa ne ya sakko daga cikin idanunta,da kallo Aryan yabi bayan Jalal yana jin babu daÉ—i a ransa,kallon Jalilerh yyi yace “sorry beb,Æ™ilan laifi kikai masa go and apologize him” kaita gyaÉ—a nasa cike da Æ™uruciya a hankali ta nufi part É—in nata cike da tsoro, Jafar daman ko takan Jalal baibi ba sbd badan shi yanzo gidan ba, bobo na shiga part É—insa ya shiga cikin bathroom ya sakarwa kansa shower,ruwan na dukan jikinsa yana sakin ajjiyar zuciya, Abbou bai shigo gida ba sai sanda ya gama abinda zaiyi a waje shida Alhaji Kamal (am so sorry nayi miskate mai maÆ™on nace Alhaji Kamal,sai nace Mubarak, but president Mubarak daban, Alhaji Kamal kuma abokin Abbou dat all).
cikin kayan bacci marasa nauyi ya shirya kana ya fesa turare masu Æ™amshin gske,bayan ya kammala yaja system É—insa ya fara dannawa, Jalilerh tun É—azo take tsaye a bakin Æ™ofar parlour’n sa amma tsoron shiga take sbd bata san mene zai mata ba,bayanta ta juya taga Imran murmushi yyi mata yace “a’a bebn uncle ki shiga mana” kaita gyaÉ—a masa kana a hankali ta tura kanta cikin parlour’n ajjiyar zcy ta sauke,cikin nutsuwa kuma ta Æ™ara tura kanta cikin bedroom É—in hango shi tayi Æ™wance a kan bed yaja duvet ya rufe jikinsa,wajansa ta Æ™arasa tare da tsayawa a kansa,a hankali cike da tsoro kuma tace “uncle” ta faÉ—a tana turo bakinta gaba, lumshe idanunsa yyi tare da juyowa ya kalleta, É—auke idanunsa yyi ba tare da yace mata komai, shassheÆ™ar kuka ta fara kafin ta Æ™ara kiran sunansa,a É—an hasale ya kalleta yace “what..?” Æ™ara sautin kukanta tayi ba tare kuma da yace komai ba yaji ta faÉ—a jikinsa tana kuka, lumshe ido yyi yana jin kansa na Æ™ara sara masa,ga kuma kukan da take masa a kunne,cikin Æ™asa da murya yace “sorry me Uncle yyi mki?” cikin kuka ta É—aga kanta ta kallesa kafin ta kifa kanta a Æ™irjinsa tace “ba kai ne bakai min irin na sister Nihila ba” waro ido yyi waje yace “me..?” hannu tasa a bakinsa sannan ta É—ura saman kanta,hannu yasa ya dafe kansa tare da mirginata ta gefe ya É—an É—ura Æ™irjinsa saman nata yace “ohhyaa haa bari nai baki mai Æ™yau..
Da sauri Jalilerh ta miÆ™e tsaye bata bare ta Æ™arasa jin maganar ba,ita dai tasan bata san wani abu wai shi kishi ba,haka nan kuma bata da wata alaÆ™a da bobo,ta nayi masa kallon helper,wanda ya taiamaketa,amma mene yasa ta kejin haushin abinda Nihila ke faÉ—i a kansa, jikinta taja zuwa upstrais ba tare kuma data Æ™ara cewa komai ba ta shige ta barsu zaune a wajan,jin shurun yyi yawa yasa Nusaibat faÉ—in “ina jinki” ta Æ™are maganar tana danne kukan daya tawo mata,shuru Nihila tayi kafin ta É—auki glass cup wanda ke É—auke da ruwa mai sanyi ta shanye,kallon Nusaibat tayi tare da sakin murmushi tace “Naji tsoro sbd banyi tunanin abin ba,daga baya kuma sai naji dÉ—i” kallonta Nusaibat tayi tare da dai-dai ta nutsuwarta tace “daÉ—i kuma?” kai ta gyaÉ—a mata tace “Eh! sbd bayan ya sanya bakinsa cikin nawa,sai na kallesa shima ya kallan a hankali kuma ya cire nasa bakin kafin yaja ajjiyar zcy cikin Æ™asa da murya yace “ban son surutu dat why na rufe bakin” ya faÉ—i hakan yana sakina,ina nan zaune a É—akin ina son tambayarsa amma tsoro ya hanani a haka har bacci ya É—auke sa, miÆ™ewa nayi na fara gyara masa part É—in nasa ya rage bed É—in ne kawai ban gyara, Nusaibat rayuwar bobo akwai É—aure kai idan yana wani abun sai kaga kamar mai aljanu,ina jin tsoro sosai kuma inajin tausayin sa,sbd ba kowa yasa damuwarsa ba,kamar yadda nima ban sani ba kawai dai ina harshashe ne,bobo bai son jama’a su fahimci rauninsa domin yana ganin kamar tawaye ne a rayuwarsa.
miÆ™ewa Nusaibat tayi tana kallon Nihila tace “nizan huce amma zan dawo domin yanzu na zama Æ´ar gida” dry Nihila tayi itama ta miÆ™e tsaye tana faÉ—in “ok any time ur wlcm dear” sallama tayi mata sannan tabar gidan zcyarta babu daÉ—i,Bobo na shiga cikin bathroom É—in Mameey a hankali ya Æ™arasa gaban mirrow’n ta ya Æ™urawa kansa idanu kamar mai nazartar wani abu,kamar yadda yake tsaye haka wani hayaÆ™i ya fara fita ta cikin madubin zuwa kan fuskarsa,cikin abinda bai huce 20 seconds ya fara tari wanda ya haifar da zubuwar wani jini ta cikin hancinsa da bakinsa,jinin na zuba hayaÆ™in na É—auke wa, lumshe gajiyayyun idanunsa yyi cikin ransa yake kiran sunan Allah domin ya kawo masa É—auki,wajan sink ya nufa ya wanke bakinsa zuwa fuskarsa bayan ya gama ya buÉ—e Kofar ya fito,yana fitowa Mameey na shigowa cikin parlour’n kallonsa tayi da alamun tambaya a fuskarta kafin tace “Jalal yanzu akace min kana part É—ina,so na duba ko ina baka ciki ashe kana bathroom lfy dai? domin ina kula dakai duk wajan Æ™wana biyu saika shigo bathroom É—ina bayan aÆ™wai bathroom a side É—inku,kallonta yyi ya É—auke kai kafin yace “Mameey barka da yamma” murmushi tayi masa domin tasan tunda yace haka bazai taÉ“a amsa mata tambayarta ba,”yawwa Jalal,ya shirye-shiryen fara zaÉ“an cikin gida?” zama yyi saman sofa tare da lumshe idanunsa kafin yaja numfashi yace “Mameey an kusa,matsala É—aya ake samun daga É“angaren wasu gwamnoni guda uku wanda suke marawa Mubarak Yahya cibo,amma in sha Allah komai zai dai-dai”ya faÉ—a yana miÆ™ewa tsaye,da farin ciki saman fuskartar tace “ah ma sha Allah mutum uku babu abinda zasu hana ai” kai ya jinjina yace “ai kam” yana faÉ—in hakan ya fice,a main parlour ya samu Abbou dawowarsa kenan daga yiwa wata mata operation, Abbou na ganinsa ya zauna akan sofa yace “Bobo gobe Uncle É—inka Lamir g zai dawo kasan cewa baya jam’iyyar D.R.P ta C.P.P yake kuma shine na hannun daman President Mubarak Yahya cibo,so bansan yadda zai É—auki lamarin ba,ina tsoro ace an samu matsala dashi” kallonsa Jalal yyi yace “Abbou kada kadamu ita siyasa haka take ai,kowa da ra’ayinsa ina ganin wannan ba matsala bace” kai ya gyaÉ—a yace “yaushe rabonka da zuwa gidan Alhaji Kamal” haÉ—e fuska Jalal yyi yace “na manta” Mummy dake sakkowa tace “tun kana yaro dai” kwaÉ“e fuska yyi domin daman abinda bai son ya faÉ—a kenan, miÆ™ewa Abbou yyi yace “kaje yau basai na sake magana ba” yana faÉ—in hakan Abbou yaja hannun Mummy sukai upstrais shuru yyi bai Æ™ara magana ba kamar yadda Abbou bai Æ™ara cewa komai ba.
da daddare bayan ya dawo gida daga meeting É—in da sukai ya shige part É—insa yyi wanka ya sauya kaya zuwa wani farin yadi mai manyan zane,Black cap ya saka tare da sanya Black cover shoe ya fesa turare,yana gamawa ya fito,yana zuwa main parlour Mama tace “yawwa irin albarka,wanda ya sha Nonon albarka, daure ka siyomin tsire wlh yau tun safe nake sha’awar cinsa kamar mai yaron ciki, zcyata sai tashi take” kai ya É—auke daga kallon Jalilerh wacce take sanye da riga da wando gashinta an rabashi gida biyu ansaya masa stone,ya sakko har wuyanta ta zama kamar wata Æ´ar baby, yace “da sauranki tunda zucyar har yanzu tana jikinki” miÆ™ewa tayi tace “daman na sani bana da wani gata a gidan nan,da Lamir yana nan babu abinda zan nema wajansa yaÆ™i,kai amma dai bakai halin Æ™warai ba,atooo rowa dai babu Æ™yau kuma wanda kaba yar shine rabonka wanda kaci kuma kashinsa zakai” ta Æ™are maganar tana sauya fuska tace “nina san da wasa kakemin domin kana da zcyar tausayi ba kamar waccen yaron da yake tafiya kamar zai kifa,kai aini jiya naga daÉ—in Æ™iba a talabijin kana jin na baka lbr…,” da sauri ya miÆ™e yace “a’a zan siyo maki riÆ™e labarinki” da sauri Jalilerh ta sakko daga saman sofa ta karaso wajansa tace “uncle zani”baice mata komai yyi tafiyar,daga saman upstrais Abbou yace “my dear bisa mana”tana jin haka tabi bayansa da sauri yana Æ™oÆ™arin shigewa cikin motarsa yaji ta kama hannunsa,zame hannun yyi tare da sakar mata ranÆ™washi a kanta da sauri tayi Æ™asa ta durÆ™oshe a wajan tana kukan,kafin yyi wani yunÆ™uri Aryan ya Æ™arasu wajan tare da sanya hannu zai taÉ“a Jalal ya sanya hannunsa gaba É—aya ya É—auketa zuwa cikin motar yana zuwa ya cilla ta a side É—in gaba shima ya shige mazaunin drever,baiko kalli inda Aryan yake ba sai da Aryan É—in yace “yaya daman wasu matasa ne sukeson ganawa dakai gobe,amma ban basu dama ba sbd naga kana busy,sannan wasu Æ´an jarida ma sun turo katin gayyatar ka zuwa gidan t.v É—insu domin su tattauna dakai akan takarar daka fito” lumshe idanu yyi yace “matasa san kace gobe suje gida gona ina can,su koma gidan t.v kace sai week end” yana faÉ—in hakan yaja motarsa ya fice daga cikin gidan,kai tsaye wani restaurant ya nufa mai suna vip restaurant yana zuwa yyi parking a parking space ya fito,hannu tasa zata fito taji ya kulle Æ™ofar,dole ta zauna ciki tana kumbure-kumbure,kai tsaye cikin restaurant É—in ya shige yana shiga ma’aikatan wajan sukai masa barka da zuwa tare da bashi kujera”no ba zama zanyi ba” oder ya basu yana bayarwa yace akai masa mota yana faÉ—in hakan yyi gaba abunsa,yana gaf da shiga cikin motar yaji ana faÉ—in “Assalamu alaika”
juyawa yyi a hankali ganin macace yasa ya É—auke kansa gefe guda kafin a hankali kuma yace “Wasalamu alaiki” yana faÉ—in hakan ya shige cikin motar yana jiran a kawo masa oder da yyi, Æ™ara Æ™arasuwa jikin motar tayi tare da sunkuyar da kanta dai-dai saitin Kofar motar tace.
“Allah yasa ban katse maka hanzari ba,nayi tunanin rabuwa dakai ganin kamar sauri kake amma zcyta taÆ™i amincewa da hakan,ina fatan zaka fahimce ni”
Jalilerh take motar ta É—ago kanta a hankali kuma tayi Æ™asa da muryarta tace “who is she?” kafin ya bata amsa Hibba tace.
“i”m Hibbatullah Mubarak Yahya cibo,kuma ina sha Allah am going to be ur Aunty soon”
É—auke kai Jalilerh tayi bata sake magana ba,sai wayar bobo ta taci gaba da dannawa tana game.
numfashi ya sauke kafin yace “ok thanks,the You want me to help you?” ya Æ™are maganar yana Æ™wace wayarsa daga hannun Jalilerh sbd kada tayi masa restore, murmushi Hibba tayi kafin tace.
“Kawai ka birgeni ne tun a wajan siyan mota,nai ta binciken inda zan sameka sai gashi yanzu Allah ya haÉ—amu,idan babu damuwa ina son sanin sunanka?”
horn ya danna a motarsa wajan 10 seconds ya kalleta yace “Muhammad Jalal bobo” É—an waro idanu tayi haka nan taji kamar ta taÉ“a jin sunan but at where? shine abin tambayar amma ta manta, murmushi tayi tana juya fararan idanunta tace.
“wow!! nice name bobo, please can u give me ur contact? sai mu dinga gaisawa as frnds,kallon Jalilerh yyi yaga gaba É—aya ta É—auke kanta tana kallon waje,hannu yasa ya É—aukota gaba É—aya ya ajjiye ta saman cinyarsa kafin yace.
“ina da mata”da mamaki take kallonsa sai taji duk zcyarta babu daÉ—i ranta ya É“aci,saita kanta tayi tace “mata kuma..?wace?” rungome Jalilerh yyi wacce tai Æ™wance a jikinsa ta fara bacci sbd sanyin a.cn É—aya shigeta yace “gata” saurin riÆ™e Æ™ofar motar tayi sbd jirin da taji yana neman ka da ita,cikin nuna itama idanunta a buÉ—e yake tace “haba wannan yarinyar,ai sai dai Æ´arka badai mata ba,idanma matarce ka rasa wacce zata aura sai kwaila mara jiki sosai” kallon gefen idanu yyi mata sannan ya kalli Jalilerh wacce ta É—an ware idanunta tana sauraran maganar tasu sama-sama,wani smile yyi sbd shi gare shi bai ga wani banbanci ba,shekaru kawai zata nunawa Jalilerh da kuma girman jiki,amma duk halittun da zai nuna Jalilerh macace ya gama bai yana sai Abinda ba za’a rasa ba, Æ™asa yyi da kansa dai-dai fuskarsa Jalilerh yace “haaa ba kinki na baki sweet kinji Noor” cikin magagin bacci ta buÉ—e bakinta,a hankali shi kuma ya sanya bakinsa cikin nata tare da bata wani lafiyayyan kiss,kafin tayi wani yunÆ™uri ya zoba mata yawon bakinsa cikin bakinta, lumshe ido tayi tai lamo jikinsa a hankali kuma baccin yyi gaba da ita.
baya Hibba tayi cikin Æ™aramin lkc mood É—inta ya sauya,kafin tayi Æ™arfin halin faÉ—in “na yarda,amma kada kayi tunanin shkkn komai na iya sauya” tana faÉ—in hakan ta shige cikin motar ta,sai a lkcn aka kawo masa oder da yyi shima ba tare daya tashi Jalilerh ba ya gyara mata Æ™wanciyar tare dayin revers yywa motar key pouting lips É—insa yyi tare dayin bisimillah ya fara dreving.
basu isa gida ba sai wajan Æ™arfe 9 na dare sbd wani waje daya tsaya sukai wani É—an Æ™aramin meeting aÆ™an zaÉ“an cikin gida,yana shiga Mama tayi saurin miÆ™ewa tsaye tace “ina nan zaune,ka ganni sau goma kenan ina sheÆ™a amai,duk yadda akai Æ™wantaccen cikina keson tashi”waro idanu yyi kafin ya miÆ™a mata leda É—aya acikin ledojin guda biyar É—in daya shigo dasu, kafin yace komai ta yaga leda tayi zaman dirshen a Æ™asan carpet tace “ma sha Allah gashi kowa ya sha kayan haÉ—i wannan É“oye shi zanyi sbd É“erakun gidan nan” baice mata Æ™ala ba ya haura saman upstrais hannunsa riÆ™e da Jalilerh wacce take ta bacci abinta,cikin nutsuwa ya tura Æ™ofar bakinsa É—auke da sallama,shuru Nihila tayi harya Æ™arasu cikin bedroom É—in ya Æ™wantar da Jalilerh yaja mata duvet ya rufe mata jikinta dashi,kallon Nihila yyi yace “zo nan” miÆ™ewa tayi taga ita sai Æ™aramin wando da rigar bacci mara nauyi, hannu yasa ya murÉ—e mata kunne yace “baki amsa sallama ba ko?ko baki san muhimmancin ta bane?” turo baki tayi hawaye na zuba a saman fuskar ta tace “shine kuka tafi kuka barni, tun ka dawo baka taÉ“a fita dani ba,ko kafi sonta akaina”baki ya Æ™ara murÉ—e mata kafin yasa hannu ya jata zuwa jikinsa yace “ban son irin wannan kalaman,ke jinina ce,ita kuma Æ´ar uwata ce kowa da matsayinsa” ya faÉ—i hakan yana share mata hawayen fuskarta yace “babyn Mummy ta girma bata san ta girma ba eyeee” ya faÉ—i hakan yana sumbatar goshinta yace “make sure kinyi maku addu’a keda ita” kaita gyaÉ—a masa ya fita yaja masu Ƙofar da sallama ya shiga part É—in Mameey ya sameta tana shirin fita kasan cewar itace da girki, “Mameey Barka da dare” murmushi tayi tace “yawwa babban yaya” ledan hannunsa guda biyu ya miÆ™a mata yace “ke da Abbou” gdy tayi masa tare da addu’a kana ta nufi part É—in Abbou,shima wajan Mummy ya shiga ya sameta zaune tana kallon wani abu,tana ganinsa ta É“oye a bayan pillow,zama yyi yace “sannu Mummy na” sumar kansa ta shafa tace “yawwa yarona,sannu kaji bobo kaga abinda banso kenan harkar siyasa ya fara saka gaba” miÆ™ewa yyi yace “kai Mom” ya faÉ—a yana bata ledan hannunsa yace “goodnight” ok “take care” yana sauka dwonstrais ya samu duka samarin gidan gaba É—aya suka haÉ—a baki wajan faÉ—in “sannu yaya” zama yyi yace “yawwa darling” kallonsa Aryan yyi yace “tun É—azo nake saka ran ganin dawowarku ashe sai yanzu,bari naje naga beb ko batai bacci ba” fuska babu yabo babu fallasa yace “sunyi bacci” ba dan ran Aryan yasu ba ya zauna, Irfan ne yyi dry yace “da dukkan alamu anyi gaba da zcyar wani” da sauri Imran yace “koba Aryan ba..?aina kula tunda ya sanu bbyn yaya ya faÉ—a” murmushi yyi yace “wlh ina sonta,kuma ina da burin auranta” miÆ™ewa Jalal yyi tare da basu ledan hannunsa guda É—aya wacce ta kasance babbar ciki,yana basu yyi shigewarsa part É—insa.
zaune president Mubarak Yahya cibo yake yana kallon matarsa Haj Ayshert yace “bana barin dukkan wanda yace zai yi takara dani akan abinda na keso,na É—auki alwashi wulaÆ™anta dukkan wanda yace zai hakan,kuma zan tabbatar masa da magana ta gsky ce,badai na tura masa da saÆ™o ta email É—insa akan ya janye takarar ba yaÆ™i,shi É—an miskilin tsiya ko..?” ya faÉ—a yana fesar da numfashi ta cikin bakinsa,cikin girmamawa Haj Ayshert tace “your Excellency you don’t need to worry about this issue,shekararka 4 kana mulki ya kamata ka hqr haka tunda babu abinda muka nema a rayuwa muka rasa,daman ita siyasa ai ba’ar dugaro bace,kuma ba gado bace bare ace dole mutum yyi sorry I don’t mean to hurt u” miÆ™ewa yyi yace “ban shiryar barin siyasa a yanzu ba,kamar yadda nayi al’Æ™awari sai nayi shekara 8 cif akan mulki, shima da ina da iko sai na Æ™ara juyawa,dan haka dukkan abinda za kice kin daÉ—e baki faÉ—a ba,ruwanki ki maramin baya kisa a zaÉ“eni ruwanki kiÆ™i,kuma zuwa yamma Lamir zai dawo kuma nan zai fara zuwa domin nike da buÆ™atar ganinsa,dukkan hanyar da za’a bi a kawar da wannan mutumin a duniya sai nayi kuma ta hanyar Lamir zan iya hakan..²⁸,²⁹
