SIRADIN RAYUWA CHAPTER 14 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 14 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 14 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA Ko sau daya bata taba tuhumarsa ko sake tunkararsa da maganar ba,domin yabar maganar tun daga ranar data bashi zabi,ya kuma zabi yi mata biyayya,ya zabi ya faranta mata,ya zabi yabi abinda ta shimfida ta kuma tsara. Bata manta irin wahalar da yasha a sannan shekaru bakwai baya,har hakan yaso karya zuciyarta,yaso yasa ta karya tsarin nata da hannunta,ya kusan sanyata ta maida hannun agogo baya ta kuma sauka daga kujerar naqin data hau,saidai daga baya ta qarfafawa kanta gwiwa,taci gaba da zama kan matsayin da take kai,duba da abubuwan da zasu biyo baya idan har ta biyewa son ran abdul’azeez din,cikin abubuwan da zata iya fuskanta din kuwa harda kunyata gaban abokan xamanta,wanda ta dade da sanin cewa bata da abokan gaba sama dasu,suna daga cikin mutane dake sahun farko farko dakeson ganin kunyatarta da tozartarta cikin masarautar. Abu mafi girma kuma dayafi wannan tsanani shine…..hukuncin da zata fuskanta daga …