SIRADIN RAYUWA CHAPTER 10 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA

SIRADIN RAYUWA CHAPTER 10 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA
SIRADIN RAYUWA CHAPTER 10 BY SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA Ajjiye wayar tayi tanajin wani daci da zallar rashin adalci cikin lamarin gaba daya,a iya sanin data yiwa fulani aishan macace mai tausayi jin qai da kuma kyan hali,batasan meya sauyata haka lokaci daya ba,tayi mamakin yadda tabari BURI gami da ALWASHIN watsa aniyar maqiya yakeson sauya halayya da dabi’arta,ta dauki buri mai tsaho da girma akan azeez fiye da yadda aka santa,duk da cewa dama can mutum ce mai son ‘ya’ya,amma duk da haka tana da kyakkyawar halayya da dabi’a wadda ta siya mata soyayya mai girma a zukatan al’umma,sai gashi yanzun tana wasu abubuwa da suke baiwa sodangi mamaki,halayyar da sam tasan ba tata bace,rashin adalci,rashin tausayi da kuma nuna halin ko in kula akan kowa face diyoyin cikinta,indai hakane kuwa maqiya sun cucuta,dafin magauta ya ratsata,ya mata kuma tasiri da har yafidda kyakkyawar halayya daga cikin jininta ya sauya mata wata.       Kamar yadda ta zata din kuwa babu wanda ya kalla abincin ma a c…