RAUDHA CHAPTER 2

RAUDHA CHAPTER 2
RAUDHA CHAPTER 2 _______?Su Saude dake zaune suna kallo a wayan Larai suka ɗago kai dasauri suna kallon RAUDHA, ko waccen su nan da nan tashiga hankalin ta coz sun san bata shigowa cikin ɗakin su idan har ba wani laifi sukayi mata ba, shanyayyun manyan idanuwan ta tasauke akan su tana bin su da kallo, sai da tagama ƙare musu kallo cike da isa tace+ “Uban me kuke yi da har zan kira ku ku kasa amsa min?” Zuru-zuru sukayi da ido suna kallon ta, sai Larai ne tayi ƙarfin cewa “Kiyi haƙuri Hajiya wlh bamu ji bane”. Dogon tsaki taja tace “ki shirya kizo in aike ki supper market”. Idanunta dake kan Saude shiyasa tagane da ita take yi “To ranki yadaɗe”. Cewar Saude tana miƙewa dasauri Ita kuwa juyawa tayi tafice tanufi ɗakin ta, bata daɗe da zama ba Saude tashigo, kuɗi tamiƙa mata tafaɗa mata abinda zata siyo mata tafice, wayan ta taɗauka takira Ramcy, ringing ɗaya taɗauka “Ramcy kibar aikin nan kawai”. Cike da mamaki Ramcy tace “meyasa?” RAUDHA tace “na sauya shawara ne, zan kira ki anjima yanzu zan fi…