ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir
ZUMUNTAR KENAN CHAPTER 6 by Sumayyah Abdul-kadir mana ziyara. Momin ABU rungume da sabon baby dinta kyakkyawa kamar Baban ABU, na rungume shi na rasa inda zan sa kaina don farin ciki. Bakina kamar ya yage don fara’a ina rungume da babyn, na ce, “Wai ya ya sunansa Momi?” Ta ce, “Ban sani ba, ni fa ba wurinki na zo ba Aku sarkin magana’”’. Na yi narai-narai da ido kamar zan yi kuka. Yaya Hauwa ta ce, “Rabu da ita Fa’iza, sunan shi Baban Kaduna (Mukhtar) shi kenan?” Na ce, “To, Ya Hauwa ya zamu ke kiran shi?’ Ta ce, “Kowa a gida yana ce mishi ‘WALID’. Dadi ya rufe ni, na ce, “Yeh! Mun samu Waleed da Waleeda”’. Ta fannin Fa’iz karatun Diploma a Kaduna Poly ya sha masa kai, a kokarinsa na hattama (ND) wato National Diploma. Fa’iz wani irin mutum ne da baya son karatun boko sam. Diplomar ma sai da suka takura masa su Baban ABU suka bude mishi wuta, don bayan kammala sakandire dinshi a Madina kin ci gaba ya yi, kai dai barshi da tukin mota. Duk wanda ke son zuwa unguwa Fa’iz ne direbansa, ba …