ZABIN SAMHA CHAPTER 6

ZABIN SAMHA CHAPTER 6
ZABIN SAMHA CHAPTER 6 Karan karfen dataji ya sauka a kasa ne yasa Samha ta bude idanunta. Ganin abunda yake faruwa a gabanta ne yasa ta kara zaro idanu. Sabah ta gani ya cakume kwalar Zack sai faman zabga mishi naushi yakeyi ta ko ina yana fadin “Bakada hankali ne Zack? Kasheta kakeso kayi ne ko me? Toh idan daman kana rike dani ne a zuciyarka to ka fito filli ka tunkareni ba wai ka biyo takanta ba”. Sabah ya karasa maganar yana cigaba da kai mishi duka da naushi ta ko ina. Zack dayaji duka, azaba iya azaba ya bude baki a wahale ya soma fadin ” Aliyah ta taso tun muna yara tana dawainiya da sonka har zuwa yanzu amma kai ko ajikinka. Meyasa bazaka sota bane eh?” “So kake na sota saboda inajin tausayinta ne ko meye?! Ana so dole ne wai?!” Sabah ya tambayeshi a tsawace. “Kai kadai Aliyah takeso, ka tausayamata ka sota ko da kadan ne”. “Toh baza’a sota din ba. Kai har waye da zaka bude baki ka fadamun abunda ya kamata naso? Me ka sani game da so?”. Sabah ya tambayeshi yana zaro mishi idanunsa …