RAYUWAR ASMAU CHAPTER 5
RAYUWAR ASMAU CHAPTER 5 Pretty ce zaune a gaban wani boka. Kai sufar bokan ma kanta abar kyama ce da tsoro bare kuma warin da yake yi.+ Abinda take bukata ta gama fada masa. buga kasa yayi yai dube duben sa sannan ya ce, “Kin kawo aiki me wahala dan mutanen nan ba a zaune suke ba wajen ibada sai dai zan san yadda zamu yi muga ta wacce hanya zamu bi.” “Yauwah ni na fi so ma ita yarinyar a haukata ta yadda dole zai hakura da ita ko ta mutu ma.” “Kull!” Yai mata wata tsawa ya ce, “Wannan yarinyar har tafi Aslam tsari da riko da addini baza mu iya da ita ba. Tafi karfin mu.” Da haka ta zube masa kudi masu waya sannan sukai akan nan da wata daya ta dawo. Daga nan ma Pretty ba gida tayi ba wajen wani bokan ta karayi suka karai mata alkawarin komai zai wakana yadda take so. Da haka ta koma gida da murna abinda take so zai zo gare ta. Dan har ta fara shirye shiryen auren ta da Aslam. Aslam kuwa bai son wainar dake soyawa ba. Shi dai bai da buri da muradin da ya wuce ya ganshi tare da Asma’u. Kowa da yasan …