SOYAYYAR MU CHAPTER 4
SOYAYYAR MU CHAPTER 4 A yau Aliyu zai yi tafiya zuwa Abuja, tafiyar kwana uku don kammala shirye shiryen taron bude sabon kamfanin shi da aka gama ginawa. Ammi tsaye a gaban durowar kayan shi tana hada mishi kayan da zaiyi tafiya da su yayin da shi kuma yana bisa gadon shi yana shigar da wasu saqonni a laptop. Ammi tace “Allah dai ya kaimu bikin ka da Hanifa ta cigaba da hidima da kai” Murmushi yayi yace “idan zata iya ba” Ammi ta gane me yake nufi don haka ne tace “ai ta fara koyon yadda zata zauna da kai baby na” Wani bangare na durowan shi ta kalla tace “yanzu Aliyu manyan kayan da ka dinka gaba daya gasu nan babu wanda ka taba saka wa? Wai yaushe zaka girma ne?” Dariya yayi yace “yi haquri Ammi zan sa, wadannan ma zan bada su sai in dinka wasu tunda naga kaman sun dan kwana biyu ko?” Cikin mamaki ta waigo ta kalle shi tace “zaka bada su dukda baka taba sakawa ba? Ka dinko wasu suma ka ajiye su cikin durowar? Wato dai idan ba qananan kayan nan ka sa ba baka jin dadi ko? Allah ya shirye ka…