SOYAYYAR MU CHAPTER 2
SOYAYYAR MU CHAPTER 2 WANENE ALIYU? Alhaji Bashir kankia ya kasance attajiri kafin Allah ya dauki ran shi da matar shi Hajiya Nafisa. Kafin su rasu sun kasance da yara uku ne a duniya, Alhaji Ibrahim shine babba sai mai bi mashi Alhaji Muhammed sai autar su Hajiya Mariya. Su Ibrahim sun kasance yara masu gata a rayuwa, sun samu ilimin boko da na addini mai zurfi, ko kafin mahaifin su ya rasu sun riga sun tara dukiya tasu ta kansu. Bayan mutuwar mahaifin su ba da dadewa ba ita ma hajiya Nafisa ta rasu. Su Alahji Ibrahim sun yi rashi na iyaye amma ba rashi na kudi ba domin sun gaji dukiya mai tarin yawa.+ Alhaji Ibrahim ya auri matar shi Hajiya Halima wadda aka fi kira Mummy, Mummy mutumiyar Katsina ce, yaran su uku. Amina, Mustapha da auta Muhammad Kabir. Alhaji Ibrahim yana da gidaje dayawa a cikin garin katsina da Kaduna. yana zaune a daya daga cikin danqararrun gidajen shi dake nan cikin GRA ta Katsina. Alhaji Ibrahim yayi aikin banki a bankin Zenith Bank, sai da ya kai…