MATAR SHEIKH COMPLETE

MATAR SHEIKH COMPLETE
MATAR SHEIKH COMPLETE SOMIN TABI.( something like_prologue or so??).4 2014. Kano, Nigeria. Kallon kwalaben da ke gabanta tayi amma bata iya karanta komai daga jikin su. Idanunta sun kada sun yi ja wur, kanta har wani juyawa yake tana ganin abubuwa uku uku. Hannu tasa ta dauki wata kwalba da babu komai a cikinta, ta bude wata da bata ma iya karanta sunan ta zuba rabi a kwalbar da babu komai ta ajiye hannun ta na rawa. Wata kwalbar ta bude ta hade da wancan rabin ta jijjiga sannan ta shanye duka. Cikin mintuna kadan ta sake buguwa sosai kasancewar magungunan sun ratsa mata jiki sosai. Duk da a yanayin maye ta ke, tana iya tuno dalilin da yasa ta fara shaye-shaye. Zafafan hawaye ne suka zubo daga idonta tana dana sanin rayuwar ta. A haka dai tana tunane-tunanen hankali da shirme da ma wanda magungunan ke kitsa mata su, bacci ya dauke ta. **** Hoton dake hannunsa ya ajiye yana ajiyar zuciya. Har izuwa yaushe ne zai manta da matar sa, Jamilah? Anya zai manta da ita kuwa? Jijiga ka…