ZUCIYA CHAPTER 21
ZUCIYA CHAPTER 21 Da yamma Dan litti ya kawo mai mota, bai bari ma sun gaisa ba makullin kawai yaba mai gadi ya juya yai gaba.+ Suma wajen karfe 6 suka fito daga gidan, hannunsu rike da juna, tana dan dingisa kafa kadan kadan. Tuki yake zuciyarta nata sarka masa abubuwa kala kala, Nafi kam ganin haka yasa ta kwanta kawai batace komai ba. Sunje shiga gida ya zaro Atm daga wallet dinsa ya mika mata. Kallansa tai tace ” Name nene?” Yace ” nasan akwai abinda kike bukata sai kuje ke da Little, sannan ki barshi a gunki incase in akwai abinda zaki bukata nan gaba.” Kallan mamaki tamai tace ” nan gaba in zan nema ba sai na fadama ba?” Kansa yad’auke baice komai ba. A karamar purse dinta ta saka suka shiga gida. Sunje gun ajiye mota sukaga Anisa da su Umma a tsatsaye sai masifa akeyi, ga Asim nan ya rike kofar motar Anisa shima yana fada. Tunda suka kula da motar Ashraf sai duk suka zubama ma motar ido kowa fuskarnan a murtuke, Nafi kam yau ko a jikinta jitake yanzu bazata i…