ZUCIYA CHAPTER 14

ZUCIYA CHAPTER 14
ZUCIYA CHAPTER 14 Shiru sukai can Nafi tace ” Little to ai shi Mahaifin Yaya bai sani ba na tabbata daya sani da bazai ci amanar kaninsa ba.” Little ta kalli Nafi tace ” A ido Abbana yana nuna komai ya wuce sai dai daga yanda al’amura suke tafiya a gidan nan banaji har a wannan lokacin da Mumy take matarsa ya yafema Abban Ashraf.”+ Cikin mamaki Nafi tace ” To ita Mumy me yasa ta aureshi daga gama takaba?” Little ta d’aga kafada tace ” Allahu a’alam shiyasa sam haryanzu Yaya bai sako ba.” Nafi tai shiru tana tunani, little tace ” kuma kinsan ba wanda ya fad’ama yaya mumy ta auri Abba na? Shikuma a lokacin baiyi hankalin da zai kawo komai ba har sai sanda Mumy ta haifeni, lokacin shi kuma hankali ya fara zuwa mai.” Nafi ta zaro ido cikin mamaki tace aikam ba’a kyauta ba, amma meyasa Mumy tai haka?” Little ta girgiza kai alamar bata sani ba.” Nafi ta daure tace ” To naji ana zancen wasiyya har ga matarsa?” Little ta share kwallarta tace ” Feena akwai wani sirrin da Mahaifin Yaya ne kawai…