GANGAR JIKINSA NA AURA COMPLETE

GANGAR JIKINSA NA AURA COMPLETE
GANGAR JIKINSA NA AURA COMPLETE GANGAR JIKINSA NA AURA Chapter 1 Wata kwarababbiyar mota kirar bus mai karar fatattakekkiyar salansa ce ta tsaya a bakin get din makarantar yan mata ta gwamnatin tarayya dake garin Kazaure, wato F.G.G.C. Kazaure. Tana tsayawa kondastan motar ya ja kofar ya bude “Barararaa” saboda kwankwatsewar da kofar motar ta yi sakamakon cin ruwa da gafje-gafje da tsabar tsufa. Wani dattijo mai kimanin shekaru saba’in da doriya ne ya fito, da wata yar yarinya tana biye dashi wacce shekarunta ba zasu wuce shekaru goma sha daya ba, Bayan sun furfito kondastan motar ya zagaya baya wato but ya dauko wata katuwar akwatin karfe irin ta *yan makarantar wacce aka dafka sunan mai akwatin garza-garza da fenti baki wato HANNE HABU IMAMU. Ya ajiye gefe ya sake janyo wata karamar katifa wacce take daure ya dora akan akwatin, sannan ya dauko wani bokitin karfe sabo dal yana sheki shima an fenteshi da sunan mai bokitin wato HANNE HABU IMAMU. Daga karshe ya mayar da ko…