YANAYIN RAYUWA CHAPTER 6

YANAYIN RAYUWA CHAPTER 6
?YANAYIN RAYUWA????????? CHAPTER 6 By Halimatusadiya. Ana kiran sallah mangariba,yashigo gida a falo ya tarar da zainab da Hafiz suna kallo,dun basuma san yashigo ba. ” Bakuji ana kiran sallah bane .” A sawace yayi mgn , dasauri suka tashi zasu wuce dun yin alwala,hafiz ne ya iya cewa ” Baba sannu da dawwa.” ” Yauwa, wuce maza kayi alwala mutafi masallaci.” Wucewa hafiz yayi. After sundawo daga masjid,dukkan su suna falo suna kallo,baiga zali ba dukda bata zama tayi kallo amma bata zo tamai sannu da dawwa ba, gashi har ankusan isha bata fito ba. ” Zuwaira wai inna zaliha ne?” Baba yake tambayan mama. Dasauri tadaga ta ganshi tana milmil da ido kaman barauniya. ” Mene inna tambayan ki kina wani musulmusul da ido kaman mara gaskiya.” ” Am…am..am daman …” Se kuma tayi shiru ” Daman me?” Sun kuyar da kanta tayi kasa dun bata san me zata cemai ba. Hafiz ne yace ” Baba adda zali kam tun safe tafita dun mun dawo skull bamu same taba gashi har y…