YANAYIN RAYUWA CHAPTER 15
?YANAYIN RAYUWA?????????. CHAPTER15 By halimatusadiya saleh ( saliha)? Ba ajima ba,maryam ta shigo dakin rike da kayan zali,ba ma zali tayi, ta musu seda safe. Toilet ta wuce dun sa kayan,mom bata hanata ba, sleeping dress ne riga da wando,tana gama sawa tafito. Kallon ta mom tayi tace ” ki samo ki kwanta,da safe muyi magana.” Ba musu zali ta haye gadon ta kwanta,tama mom seda safe. Idon ta a rufe,amma bata yi barci ba,duk mom ta lura da itta amma ta basar, dakyar barci ya dauke ta. Da safe ta tashi duk jikin ta ciwo yake,haka ta daure tayi sallah,kafun tayi wanka ta shirya cikin uniform nata. Sede bata sa hijab dinba, daya ke batayi breakfast ba,a falo ta tarar da su,suna shirin yin breakfast,guri ta samo ta zauna. Dakyar take tura abincin,dun bata jin dadin bakin ta,bata dade da fara’a cin abincin ba,sega su ya Umar sun isu gun. Gaban tane yayi mugun fadowa,kujeran dake kusa da itta ya zauna,ya umar ya zauna a gefenshi. Ya …