WATA FUSKA CHAPTER 16 KARSHE
WATA FUSKA CHAPTER 16 KARSHE Maheer ya shiga damuwa sosai akan Ummul, kwana biyu ma Hafsat bata ganshiba, yana tare da Ameenu suna gabatar da wani muhimmin bincike, har sun cafke yaran Alhal Baba kusan hud’u, da Alk’awarin basu Naira miliyan goma su duka su rarraba indai suka fad’i inda take, sun samu amsar tambaynsu da wannan…..amma sesuka ci gaba da tsaresu akan sesun tabbatar an ganta tukunna zasu sakesu…….+ *************** Islam tasha mamakin yanda yae, d’akinsa taje babu alamar ya d’auki suturunsa amma babu wasu dagacikin kayan dayake amfani dasu na toilet ko wani abu makamancin hakan, babu laptop da sauran kayan aikin sa, me hakan yake nufi? Ta tambayi kanta, bame bata amsa wannan ya sanya ta juya akalar tunanin ta zuwa neman anty Nasara….. Ringin biyu ta d’aga wayar cikeda isa tacr “Sanadiyanki an hanani huld’a da kowa na zuri’ar mu, kin cuci halacci dason dana nuna miki mesa zaki kirani yanzu?” Ta k’arashe maganr da tsawa sosai “Kiyi Hak’uri anty Nasara wl…