WATA FUSKA CHAPTER 15
WATA FUSKA CHAPTER 15 Ranar maheer bashi yabar gidan Islam ba se washe gari, se zuba love akeyi ta bashi hak’uri kuma yaji dad’in hakan, yana son mutum yayi kuskure ya kuma bada hak’uri, yanda aka nanuk’ewa juna tamkar ba jego akeyi ba, shinshina da shafe shafe yashashi a wurin islam seda ta tabbatar ta gamsar dashi da wasanni tukunna ta tsiri kukan ya kwana mata, Bayason rigimar islam sukai sharad’i akan daga ranar baze k’ara kwana mata ba se Inna ta wuce, haka tace ta yarda sabida ta shrya shagaltar dashi kullum idan yazo…..wannan ma yana daga cikin shirin Anty Nasara na ganin bayan auren islam wanda ita a zatonta sone…….2 ********* Tun wuraren k’arfe tara na dare Hafsat tawa su Sophie sallama ta wuce d’akin yaa Maheer, dayike sunada Exams setaje da takardunta tana dubawa, tun tana saka ran ze dawo har bacci ya d’auketa be dawo ba, ba ita ta farka ba se asuba, tasha mamakin inda yaje ya kwana be gaya mata ba, gata acikin damuwar abinda ya samu ummul har Baba iro sunyi waya ak…