WATA FUSKA CHAPTER 11
WATA FUSKA CHAPTER 11 A hankali ya soma laluben inda ze qarajin kukan amma shiru be jiyo komai ba, yayi bincikensa sosai amma ba abinda ya gani a kitchen d’in juyawa yayi da zummar komawa d’akin har yakai k’ofar yajiyo k’arar jinjirai da k’arfin Gaske sekace wacce aka tsikara da sauri ya juyo ya kalli k’ofar store d’in kukan taci gaba dayi bil haq da iya kacin k’arfinta tamkar wacce ake ciza dukda yake kana ciwo sautin kukanne alamar bakin a toshe yake da wani abin, da sauri ya juya zuwa store ya soma binciken shi besha wahalar neman taba sabida kukan dataketa k’arayi da sauri ya zaro ta a kwalin yana huci ya kuma haska kwalin da fitilar wayarshi cinnakune a saman zanin datake kai sunkai biyar warwareta daga cikin d’ankwalin datake yayi nanma wani cinnakan ne alamar shi yake cizon ta, riqeta yayi ya soma sosa wurin a hankali yana shhhhhh alamar tayi shiru cikeda tausayawa a kafad’arsa ya d’aurata ya soma sosa mata bayan a hankali be koma d’akin ba yafi 15 mns yana sosa mata wurin …