WATA BAKWAI CHAPTER18 KARSHE

WATA BAKWAI CHAPTER18 KARSHE
WATA BAKWAI CHAPTER18 KARSHE A hargitse suka shiga asibitin. Tana ganin umman prince ishaq ta ruga wajenta tana kuka.+ Sunfi awa biyu zaune likitoci babu wanda ya fito yace musu wani abu. Hankalin kowa a tashe yake. Ko da likita ya fito kusan su duka suka isa wajenshi kaman zasu cinye shi da tambaya. Dakyar ya samu suka nutsu yace musu. “Yana hutawa ne. Ciwukan nashi anyi sa.a ba wani zurfi sukai ba. Ya zubda jini ne shi ya galabaitar dashi” Sai lokacin hankalin kowa ya kwanta. Umma tace azo a tattara kowa ya koma gida dare yayi. Su tafi da husna ma. Abar Nas kawai. Kuka husna ta saka ga shi ta kasa cewa komai. Ganin hakan yasa umma tace abar husna hankalinta zaifi kwanciya. Su duka suka zauna dakin da prince ishaq din yake. Dinkine a hannunshi da wuyanshi. Banda nan babu wani ciwo a jikinshi. Husna taja kujera ta zauna kanta ta dora gefen dagon tana riko hannun shi. Tayi kuka har fuskarta ta kumbura. Bacci kam barawo ne ya saceta. **** Hannun prince ishaq taji saman kanta. Da s…