WATA BAKWAI CHAPTER 9
WATA BAKWAI CHAPTER 9 Babu abinda yakai ciwon rashin wanda ka shaku dashi. Babu abinda yafi tashin hankali sai ya fado maka a rai muryarshi da take cikin tunaninka ta soma dishewa. Saika nemi yanda sautin dariyarshi yake ka manta saboda ya maka nisa. Ya tafi inda zakaje wata rana. Da duk yawan hawayen da zaka zubda da karin tabbacin cewa bazai taba dawowa ba. Sadaukarwa ga duk wanda ya taba rasa wani mai kusanci a tare dashi!!!*1 Tsaye yake kawai ya sakarma kanshi shower.Yanajin yanda ruwan ke bi masa jiki. Idanuwan shi a rufe. Baisan dalilin kukanta ba amman ya tsaya masa a rai sosai. Da ganin yanayin kukan yasan ko menene ba karami bane. Har ranshi dai yana fatan bashi bane sanadin kukan ta. Mutum ne shi da baya son ya takura ko a takura shi. Dan haka tun randa aka kawota sai dole suke magana. Balle daya sake kula da cewar ko magana kan dole take masa ya kara fita harkarta. Yau kukanta ya dawo masa da abubuwa da yawa. Wankan ya fito ya shirya. Fararen kayan dai ya kara sakawa…