WATA BAKWAI CHAPTER 8
WATA BAKWAI CHAPTER 8 Tun dazun da safe da tazo fitowa ta hango natacce da sauri ta koma dan bata son su hadu. Ya bala.in yin kyau cikin fararen kayan daya saka. Komai farine a jikin shi. Bata sake fitowa ba saida tai sallar azahar. Falon saman tai zamanta tana kallo. Pillow din kujerar ta dauka ta gyara ta kwantar da kanta. Kamshin natacce ya cika mata hanci. Da sauri ta zame filon ta cillar kan kujerar dake can nesa da ita. Wani yanayi takeji data kasa fassara shi. Koya maganan natacce ya fado mata sai zuciyarta tayi wata irin dokawa. Kawai kamshin shi dan naci ya tuna yanayin duminsa da maganar shi da komai nashi. Ammar! Ammar kawai! Ammar shi kadai. Haka take ta nanatawa zuciyarta ko zata daina kaita inda bata da buqata ba kuma a buqatarta. Wayarta ta dauka ta duba lokaci.Tai mamakin jan lokaci haka Kusan la.asar sai ta tsinci kanta dayin murmushi ammar ya kusan dawowa aiki. Tana wata irin kewarsa yau. Sallama taji da karfi ana kiran “Anty! Anty!! Gidan ba kowane??? Cike da…