WATA BAKWAI CHAPTER 7
WATA BAKWAI CHAPTER 7 Tunani yake in ya tafi har kano bai fada ma natacciya ba sam bai kyauta ba. Yasan ba magana take hadasu ba sam. Amman duk da hakan baya son rashin adalci. Beside zai fada matane kawai ko da wani abu ya faru. Tashi yai daga kwanciyar da yake ya fito. Ya koyi sa.a ta rage masa wahalar zuwa bedroom dinta dan tana zaune falon su na sama tana kallo. Gidan ba kaman na kano ba. Da kowa yake da part din shi. Duk da nan dinma dai part dinsu daban amman falo ya hadasu. Sallama yai mata. Yana neman waje kusa da ita ya zauna. * Kamshin shi kawai husna taji tasan ya nufota. Ta lumshe idanuwanta ta budesu a hankali. Batason fitina da yammacin nan. Cikin sanyin murya ta amsa sallamar shi hankalinta na kan t.v. Remote ya dauka da yake kan Centre table din wajen ya kashe kallon da take. Hakan yasa ta fuskantarshi. Idanuwanta a kasa. Shisa bayason mata magana sai dole. Bayason yanda take yin kaman bata son ganin shi. Kaman wata kazanta ce a jikin shi. A nutse yace…