WATA BAKWAI CHAPTER 16

WATA BAKWAI CHAPTER 16
WATA BAKWAI CHAPTER 16 Satin su biyu kenan da dawowa daga abuja. Komai na tafiyar musu yanda ya kamata. Saidai prince ishaq baya zama. Sai ya wuni baya gida wanda husna ke bala.in kula dashi a yanzun. Dan ba zataima kanta karya ba. Ta fara damuwa dashi sosai da sosai. Balle data san masu son illata shin sunfi kusa dashi a kano kan abuja. Duk idan yai cikakkun awa biyu a waje bataji ya kirata ba ita zata neme shi taji ko lafiya. * Ta idar da sallar la.asar ta sake kiran prince ishaq wayar shi har lokacin bata shiga. Tun karfe biyu take nemanshi shiru haka. Ta nemi number din Nas shima a kashe. Ta koma dakin prince ishaq din ta kwanta. Gaba daya a tsorace take. Jitai ba zata iya ba ta fito babban falo ta zauna. Num din shi ta kara nema shiru. Tai rau rau da ido. Saboda bata san wa kuma zata kira taji ko lafiya ba. Ta yanke shawarar inhar magrib tayi zata fita akaita gidansu ta dubo. Ta mike kenan ta sake komawa sama yai sallama. Batasan lokacin data karasa inda yake ba da gudu ta…