WATA BAKWAI CHAPTER 14
WATA BAKWAI CHAPTER 14 Sai daya gama kallo tsaf sannan ya juyo yace “kinada duk kayan nan na ciki? Ko nai waya a kawo” Ta girgiza kai “tace dryer ne babu irin nasu sai karami na riqewa a hannu…sai clips in nan suma babu” Wayarshi yake dannawa. “Me zakai?” Ta tambaya. Zan wayane akawo. Kamun ta sake magana harya ce “Hello…..” Hakan yasa tai shiru tana kallonshi yana bada umarnin akawo duk wani kayan da za.a samu a saloon. Saida ya gama tsaf ta ce “gentle yanda kake fadar nan sai kace saloon zamu bude” Murmushi kawai yai. Ba ai awa dayaba aka kawo kayan. Hadiman gidan suka dauke suka kai bangaren husna. Saida suka gama tsaf suka koma nasu wajen sannan prince ishaq ya miqe tsaye yace ma husna muje. Sai da taji gabanta yadan fadi. Yau akwai rigima kenan gashinta ba wani mai tsaho bane can saidai warwarewarshi ne aiki tunda rubber ne. Takan godema Allah data biyo jinin fulanin babansu ta bangaren gashi. Kanwarta taita cewa daman ita. Dan nata gashin dakyar yake parking. Ha…