WATA BAKWAI CHAPTER 13
WATA BAKWAI CHAPTER 13 Mintsininta yai a cinya bata zata ba. Tako saki wani qaramin ihu. Dan taji zafin mintsinin. Da sauri ya rufe mata baki yana zaro ido. “Shh hussy bamu kadai bane a motar fa akwai driver” Yake fadi cikin sanyin murya. Duk da akwai iyaka tsakaninsu. Ta rausayar dakai gefe tace “amman kasan da zafi aiko?” Kallonta yai ta qasan idanuwansa “umm qaramin wanda kikamin ne” ya fadi yana daga mata gira. Dariya tai sosai. Ta rasa yanda akai yake yawan sakata dariya. Tasan ammar kan sakata dariya amman ba kaman wannan ba. Yanayin yanda yake canza fuskarsa zuwa yanayin abinda yake so ne yake burgeta. Yana sa ta manta da damuwar da takanji a yanzun. Kewar ammar tana nan daram. Sai dai shi din ya cika wani gurbi da bata son da zamansa ba ma. Kallonta yake yanda tai zurfi cikin tunani. Zaiso sanin me yake yawo cikin kanta saidai shiba mutum bane mai yawan bincike. Muddin abinka bai shafe shiba yakan baka wajen da kake buqata kai taka rayuwar. Hannu yasa ya tal…