WATA BAKWAI CHAPTER 11
WATA BAKWAI CHAPTER 11 Idanuwansa kawai data kalla ya tabbatar mata da yaji kome take fada.+ Tsaye yake har lokacin ya kafa mata idanuwan na nasa da suke bala.in yi mata kwarjini. Ji take har iskar da take yawo a dakin tsaye take cik. A hankali ya tako ya qaraso inda take. Yanayin yanda zuciyarta ke dokawa ta dauka fitowa waje zatai tsabar kidimewar datai. Bata taba kawoma ranta zai kamata ba. Ko kuma zata ma ji abinda take ji yanzun idan har ya kamata. Baiko kalleta ba. Harya karaso. Hannu yasa ya zare earphone din daga kunnenta. Wayar yazo dauka takai hannu wajen. Ya hada da wayar da hannunta duka ya riqe. Jikin bangon wajen ya turata. Kalar riqon dayai mata a wajen ne yasa batai kiciniyar qwacewa ba. Idanuwansa har sun sauya saboda bacin rai. Bai taba zaton zaiji kishin wata ya mace bayan huddynsa ba. Da huddy baisan kishi kalar wannan ba. Saboda yasan shi kadaine a zuciyarta. A yanzun ma bazaice ga kalar dacin da yake ji a ranshi ba. Yama kasa mata magana. Kallonta kawai …