WATA BAKWAI CHAPTER 10

WATA BAKWAI CHAPTER 10
WATA BAKWAI CHAPTER 10 Yana kwanciya bacci ya samu. Sanda ya tashi lokacin zuhr harya gota dan haka saida ya fara yin sallah sannan ya kara yin wanka.+ Simple yadi yasa fari marar nauyi. Zazzabin daya rufe shi ya sauka sai ciwon kai kawai wanda yasan yunwa ce. Fitowa yai ya samu dakyar ya tura ma cikin shi plantain da irish. A wajen ya zauna yana dan hutawa. Jikinshi ya masa wani nauyi. * Tunda ta tashi bacci ta kunna wayarta suke chat da ammar har saida lokacin sallah yai. Data idar ma ta shirya tai tunanin fita ta duba prince ishaq. Sai taji ba zata iya shiga ba kuma. Ta zauna falon sama tana jira taga fitowarshi. Ga mamakinta daga kasa taga ya hauro sama. Murmushi yai mata da zata iya fahimta a fuskarshi kadai ya tsaya tunda tasha ganin shi yana murmushi. Mayar masa tai ta dora da fadin. “Na dauka kana baccine ai. Ya jikinka?” Saida ya karasa inda take ya zauna. Sannan yace. “Alhamdulillah. Nagode” Kamshin shi duk ya cika mata hanci. “Zan koma wajen Nas yanzun…..” Bai k…