SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 27
SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 27 Washe Gari Tun 7 Matar Abdallah ta kira Nazeefa akan maganar gyaran jiki, Nazeefa tace munanan zuwa anjuma tace Alright, tana kashe wayar, Ayyuka tadanyi sannan ta je ta sanar da iyayanta zasuje wajen gyaran jiki sukace bakomai+ Tashi tayi ta shirya sannan ta wuce gidan su Ameerah, koda taje ba wani bata lokaci sukaiba suka wuce gidan Matar Abdallah, suna shiga tace yauwa dama Ku nake jira muje ko? Nazeefa tace ba wani better ne anan gidan tana magana tana shafa cikinta, matar Abdallah ne tace akwai raguwan farfesun da mukai jiya bari na dakko maki kici kinsan Ku amare seda shan romo, Dariya tayi tace kinga matar nan kinsan komai fa, dakko mata tayi taci Ameerah ma taci suka Kora da 5alive sannan suka wuce gidan gyaran amarya! Bangaren mubeen kuwa yana wajen ginin makarantar da akemai, kirjinshi se bugawa yakeyi, Tinaninshi gaba daya yana wajen Ameerah, yanason yarinyar saboda natsuwarta, gata komai tana yinshi cikin Sanyi, Waya ya dakko…