SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 26
SILAR GIDAN AIKI CHAPTER 26 Biki nata matsowa, mahaifin Mansur yasa an gina musu gida kusa da nasu, Flat ne me 3 bedrooms gidan ya hadu matuk’a se wanda yagani+ Tunda bikin ya matso Mansur kullun yana makale da nazeefa a waya ba abunda ke rabasu se bacci shima cikin baccin to mafarkin junansu sukeyi Bangaren Mubeen kuwa, Tinaninshine ya rabu biyu yanason Ameerah amma wata zuciyar tana ka hakura da ita kawai ka nema wata, mubeen ne zaune a wajen ginin makarantar da akemai yaji bazai Iya hakuraba, shi duk abunda zai faru zaije ya sanar da ita yana sonta idan ma wani ya rigashine ya sani dan kar yai 2 zero, Daukar motarshi yayi ya tafi kofar gidan su Ameerah ya tsaya, wani yaro ya Kira yacemai please ya shiga ya ce Ana kiran Ameerah yaron yace tom Shiga yayi yaron yai sallama yace wai ance Ameerah tazo, Nazeefa suna zaune da Ameerah suna hiran yanda bikin Zai kasance “Ameerah tace Ni kuwa? Yace Ameerah akace, Amira bata yardaba dai tace ya mutumin yake? Yaron yace Farine dogo Du…