YAR MAKIYAYA CHAPTER 9 YAR MAKIYAYA CHAPTER 9 Wata sabuwa inji y’an cha cha , rashin sani yafi dare duhu ,shiyasa nace in every family akwai secret nasu amma shin Baban Junaidu zai rik’e wannan sirrin har abada? Wai ena zamu samo Suraj ne kam? Dan samo amsoshin tambayoyin nima JIDDAH nayi tattaki zuwa KADUNA garin gwamna ? ****** ******* ****** “Ya kasance sabon abu a garemu daga ni har Yaya Junaidu ganin manyan gine gine na alfarma, tabbas duniyar nan da na cikin Belel akwai banbanci ,iya rayuwar mu kiwo muka sani se gashi abubuwan da kawai a labarai muke ji yau muna ganin su. Mukan hango jirgin sama a chan sararin samaniya yayinda yake wuce wa sai kaga muna d’aga masa hannu amma yau sai gamu cikin filin jirgin sama dake Borno state. wannan sabon al’amari ne. “Na so muyi tafiya by road but gaba d’aya tun bamu je ko ina ba na gaji shiyasa na yanke shawara mu bi jirgi kawai” Cewar Mom ita de Laila Murmushi kawai tayi. KADUNA STATE. “Wow! Amma gaskiya kun shammace ni ,nayi zaton se g…