YAR MAKIYAYA CHAPTER 8

YAR MAKIYAYA CHAPTER 8
YAR MAKIYAYA CHAPTER 8 Wait!! Na san tambayar dake zukatan ku readers! Kuma nasan kuna jiran jin amsa daga *Y’AR MAKIYAYA* Well! Lets hope it’s a yay! Yanzu de Bari mu bi Suraj muji yadda zasu yi da dreamy girl d’in shi. + ****** ******* ******* Safiya ce mai d’auke da ni’ima,k’amshin sassanyar iska dake busawa kad’ai ya isa ya tabbatar da hakan. Bayan Suraj ya yi parking motar sa ya jingina jikin ta ,hannayen sa cikin aljihu ya d’aga kai yana kallon sararin samaniya, sink’in tunaninnika ne a ransa na yadda zai yi ya fara magana da Laila game da wannan al’amari ba but he has to try. Mak’e kafad’a yayi sannan ya Fara tafiya a daidai wannan lokacin ya san babu inda zai same ta in ba bakin ruwa ba don haka ya garzaya don duba ta a chan. Zaune ya hango ta a bakin ruwan tana kallon yadda yake gudana babu sautin komai wajen se na tsuntsaye da kuma gudanar ruwa , da Sallamar sa ya zauna gefen sa yayinda ta amsa tana masa murmushi, sun kai minti biyar suna zaune sun k’ura …