YAR MAKIYAYA CHAPTER 7

YAR MAKIYAYA CHAPTER 7
YAR MAKIYAYA CHAPTER 7 An ce kayi k’aryar da zata fidda kai , shin k’aryar Suraj kuwa zata yi aiki? Yaya zai yi ya shawo kan al’amarin,? In har Dad ya gano gaskiya ba k’aramin matsala zata haifar ba domin Laila bata kasance y’ar wani kawun Habeeb ba illah y’ar makiyayi mai kiwon dabbobi a saman tsaunuka. ****** ******** ******* “Who is Laila?” Dum! K’irjin Habeeb ya harba kamar agogo ,duk da yaji me Dad ya fad’a amma se yayi kamar bai ji ba ya juyo ya sake tambaya “Na’am, me kace Dad?” Mik’e wa dad yayi daga kujerar da yake zaune yace “Yes! Kaji me na fad’a who is Laila?” Habeeb yasan dole yayi acting kuma ma so fast kafin Dad ya gane komai saboda Idan yasan Laila y’ar talaka ce bazai bari soyayya ta d’aure tsakanin ta da Suraj ba ,gashi yaga irin soyayyar da suke yi dan haka ya k’irk’iro k’aryar sa yace “Dad Laila y’ar uncle d’ina ne ,kaima ai ka sani ba?” A tsare ya fad’a Amma zuciyar kam kad’an ya rage ta b’alla k’irjin shi ta fad’o k’asa duk gab’ob’in shi sun yi sanyi yana ji…