YAR MAKIYAYA CHAPTER 6 YAR MAKIYAYA CHAPTER 6 Matsowa yayi daf da Suraj gami da had’a masa lafiyayyun Marika har uku a fuska had’awa da kalmomin “Am very ashamed of you!” Harara ya watsa wa Mom cike da b’acin rai ya nufi sashen sa, Suraj na d’ago kai suka yi ido hud’u da Ameer ya nad’e hannuwan sa a k’irji ya jingina da bango yana Murmushi. Fice wa Suraj yayi a zuciye idanuwan shi sunyi jajir ,Habeeb dake tsaye cike da mamaki ganin Suraj ya fice shima ya yunk’ura zai bi bayan shi amma sai Ameer ya katse mishi hanzari ta hanyar shiga gaban sa yace “Haba d’an uwa! Long time no see! Gaskiya duk ka chanja welcome back nasan kaji dad’in zuwa Belel ko?” + Murmushi Habeeb yayi mai nuna alamar *go to hell* ya ture Ameer gefe ba tare da yace komai ba ya fice. Cikin mota ya hango Suraj kai had’e da stirring mota , k’arasa wa yayi ya bud’e motar ya shige ba tare da ya furta ko kalma ba ya zuba wa Suraj ido. Ya dad’e sosai kansa a kan sitiyarin kafin ya d’ago yayi wa mota key cike da zafin nama ya fisgo motar har sai…