YAR MAKIYAYA CHAPTER 5

YAR MAKIYAYA CHAPTER 5
YAR MAKIYAYA CHAPTER 5 Daga k’arshe Mun gano d’an giyan nan mai takura wa Laila ba kowa bane Illa *SAEED BIN Ahmad* D’an uwan Ameer , Mun ji yadda a dalilin *Y’AR MAKIYAYA* suka doki junan su har saida Ameer ya taho to the rescue, Amma tambaya a nan shine ,shin Saeed zai hak’ura kuwa? Me zai faru Idan suka yi ido hud’u da juna?. Don samun amsoshin wad’annan tambayoyi sai mu garzaya shafi na gaba + ***** ***** *******, “Suraj?” . Laila ta k’ira sunan shi tana zaune ta had’a kai da gwiwa Ba tare da ya amsa ba ya d’ago yana kallonta na wasu dak’ik’ai kafin ya taso ya zauna gefen ta yace “Fad’a min me yake damun ki, tun d’azu kin yi shiru kin had’e kai da gwiwa , wannan shirun naki har yasa na fara jin bacci” Murmushi tayi sannan ta ce “Tsoro nake ji, duba da yadda kuka yi fad’a kai da d’an uwan ka, a dalili na, ina tsoro kar nayi silar tarwatse war zumunci tsakanin ku, ina kuma jin tsoron zak’ewa a kan soyayyar ka kasancewar ka yarima gashi ni kuma y’ar makiyaya wanda bata s…