YAR MAKIYAYA CHAPTER 4 YAR MAKIYAYA CHAPTER 4 K’arisa wa tayi har inda suke ta nemi waje ta zauna kafin ta dubi Suraj tace “Kullum nakan yi mamakin dalilin da yasa kai bana ganin ka cikin y’an uwan ka , amma bayan abun da naga sun aikata maka d’azu ina tsaye daga sashen da nake se naji ba abun mamaki bane don ni kaina ban san halin wa Saeed da Ameer suka yo ba a bak’in hali, ina so kayi hak’uri My son kada ka biye musu zan yi magana da mahaifin su amma please kar na sake jin batun wai zaka koma Cairo, a lokacin da mahaifiyar ka ke fuskantar takura da tsanani bata gudu ba wa matsalolin ta ,zama tayi ta fuskance su like a lioness I want you to do the same, rise above all odds in kana son abu go for it ,in baka so babu dole yi watsi da shi like a man bana son in k’ara jin kalma irin ta karaya daga bakin d’an Auta na, live your life the way you think is right after all rayuwar ka ce hmm?”. + Ta kasance uwa mai dad’ad’an kalamai wanda tuni sukayi tasiri a zuciyar Suraj , nan take yaji a ranshi cewa koma me zai…