YAR MAKIYAYA CHAPTER 2 YAR MAKIYAYA CHAPTER 2 Duniya kowa da abunda ya dameshi, na gasgata hakan ganin yadda halayen y’an uwa uku ya sha Banban musamman Ameer wanda kowa ya shaida shi ba k’aramin magulmaci bane. Domin ganin wasu halayen na wad’annan y’an uwa dole na garzaya na kutsa kai ciki don ganin yadda zasu karb’i bak’on d’an uwansu ( *The crazy Prince*) Suraj. + **** ****** ***** Da sallama ya shiga falon yana mai cije baki cikin nuna alamar ya takura saboda jin haushin wayar sa dake sake ruri a karo na biyu. Abubakar kad’ai ne ya amsa Sallamar yayinda Saeed da Ameer suka k’ura wa takalman kaf’an shi ido baki sake, ganin yadda suke kallon shi yasa ya dubi k’afafun nashi. “Is that what I think it is?” Saeed ya tambaya cikin d’aga murya yayinda Ameer ya k’undume dariyar da taso kufce masa yace “Of course it is a cow’s dung!” Cikin d’aga murya yayi maganar kafin ya fece da dariya. “Kashin shanu fa! A ina ka samo wannan kai da yau shigowar ka gari am sure ko fita baka yi ba! Da…